Sarkin Zazzau Usman Yero

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Usman Yero Ɗan Abdullahi (1888 -1897)


Gabatarwa

Bayan cire sarkin Zazzau Malam Muhammadu Sambo, sai masu zaɓen sarkin Zazzau suka zaɓi Usman Yero daga Zuriyar Barebari suka tura zuwa Sakkwato wanda shi kuma sarkin Musulmi ya amince ba tare da sharaɗi ba, kamar yadda Ɗalhatu (2002), ya bayyana.

Amma Smith (1970), ya kawo cewa, akwai Lawal wanda shi ɗa ne ga Sambo kuma Madakinsa ta ɓangaren Katsinawa, da kuma Sa’adu wanda ya gaji ofishin Wambai daga ɓangaren Sulluɓawa dukkansu a matsayin ‘yan takara ne amma basu cancanta ba. Shi Lawal, bai dace ya gaji mahaifinsa ba wanda tsigewarasa ce ta bayar da wannan gurbin, shi kuma Sa’adu kasancewar mahaifinsa bai riƙe muƙamin sarkin Zazzau ba, wannan su ne dalilan da suka saka aka bar Yero shi kaɗai ba hammaya.

An naɗa Usman Yero a Sakkwato, sannan kuma an bashi cikakkiyar damar naɗa duk wanda yake so a ofis in banda ofishin Wambai wanda shi aka sake barinsa a hannun Mallawa.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London: Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub