Alhaji (Dr.) Shehu Idris

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji (Dr.) Shehu Idris, CFR


Gabatarwa

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris na ɗaya daga cikin manyan sarakunan Arewancin Najeriya. Mai martaba sarki mutum ne masani, sannan kuma abin girmamawa a duk faɗin arewa. Yana da karimci. Ɗaya daga ciki ɗimbin hikimomi da Allah ya yiwa mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris ita ce tafiya da mutanen a cikin mulkinsa, yakan tuntuɓi jama’a a kan abubuwan da ka-je-su-zo.

Haihuwarsa


Alhaji (Dr.) Shehu Idris, CFR

An haifi mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris a shekarar 1937. Shi ɗa ne ga Malam Idris Autan Sambo, shi kuma ɗan sarkin Zazzau na 10, Malam Muhammadu Sambo, shi kuma ɗan sarkin Zazzau na 3 Malam Abdulkarimu Bakatsine.

Karatunsa

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, ya fara karatunsa na addini tun yana ɗan shekara biyar a hannun malam Bawa da kuma malam Abubakar da ke Unguwar Iya a garin Zariya.

A shekarar 1947, lokacin yana da shekaru 11, Mai Martaba sarki ya fara karatun zamani a makarantar elimantare ta Zariya (Zaria Elementary School), daga nan kuma sai makarantar midil ta Zariya (Zaria Middle School) daga shekarar 1950 zuwa 1955. Bayan kammala wannan karatu nasa sai kuma ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina (Katsina Training College) inda ya gama a shekarar 1958.

Gogayyar Aiki


Mai Martaba Sarkin Zazzau tare da Shugaba Buhari
Hoto: Jaridar Dailytimes

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, ya fara karantarwa bayan kammala karatunsa na Katsina. Ya fara da koyarwa a makarantar firamare ta garin Hunƙuyi a shekarar 1958, daga nan kuma sai aka mayar da shi garin Zangon Aya, sannan sai Paki duk a matsayin shugaban makaranta (Head Master). Sannan kuma aka dawo da shi Zariya a matsayin shugaban makarantar firamare ta Ƙaura.

A shekarar 1960 ya zama magatakardar Sarkin Zazzau Marigayi Alhaji Muhammadu Aminu (Personal Secretary to the Emir of Zazzau). Daga baya kuma ya zama magatakardar Hukumar gargajiya >(Secretary to the Zaria Native Authority council) a shekarar 1963. Sannan kuma an yi masa naɗin ɗanmadamin Zazzau, Hakimin Birni da Kewaye a shekarar 1963, muƙamin da ya riƙe har zuwa zamowarsa sarki.

Zamowarsa Sarki

A shekarar 1975, bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu, sai masu zaɓen sarkin Zazzau suka zaɓi Mai Martaba Sarki Alhaji (Dr.) Shehu Idris a matsayin sabon sarkin Zazzau, zaɓen da ya samu amincewa daga gwamnatin Jahar Tsakiyar Arewa wacce ke da helikwata a Kaduna, a zamanin mulkin Gwamna Manjo Abba Kyari. Wannan naɗi nasa shi ya mai da shi sarkin Zazzau na 18 a jerin sarakunan Fulani, sannan kuma sarki na 3 a zuriyar Katsinawa.


Mai Martaba Sarki a Fada

Lambobin Yabo da Girmamawa

Saboda gudunmawa da ya daɗe yana bayarwa, musamman ta fuskacin kira game da zaman lafiya da haɗin kai, Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji (Dr.) Shehu Idris ya karɓi lambobin yabo da girmamawa da dama daga ciki da wajen Najeriya. Daga cikin irin waɗannan lambobi akwai digirin girmamawa na digirin digirgir (Dr.) da ya karɓa daga jami’o’in Minna (Federal University of Technology, Minna), jami’ar Najeriya ta Insuka (University of Nigeria, Nsuka), Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (Ahmadu Bello University, Zaria), da kuma jami’ar Abuja (University of Abuja) Suleiman (2016).

Sannan a shekarar 2006, Ƙunkiyar ɗalibai ta Jami'ar Ahmadu Bello (ABU Alumni Association Award) ta bashi lambar yabo ta ‘DISTINGUISHED SERVICE AWARD’, Jika (2016).

Manazarta:


Dalhatu U. (2002). Malam Ja’afaru ɗan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria.

Jika A. (2016). Categories of ABU Alumni Association Award. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://alumni.abu.edu.ng/AllCommentsSent.php? ComID=116&Mode=Advert

Suleiman A. (2016). As Emir of Zazzau Bags Another Doctorate Degree. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://thewillnigeria.com/news/opinion-as-emir-of-zazzau-bags-another-doctorate-degree/

Suleiman A. (2016). Shehu Idris: 41 Years of Purposeful Rulership. An ciro a shekarar 20016, daga shafin: http://facesinternationalmagazine.org.ng/?p=5631

Wikipedia (2016). Shehu Idris. An ciro a shekara 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Shehu_Idris


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub