Me ka ke nema?


Shafin Farko

Abdullahi Bayero Ɗan Abbas 1926 – 1953 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Abdullahi Bayero shi ne sarki na 53 a jerin sarakunan Kano kuma sarki na 10 a jerin sarakunan Fulani. Sannan kuma sarki na 3 da Turawa suka naɗa. An naɗa sarki Abdullahi a matsayin sarkin Kano lokacin yana Ciroman Kano. Shi ne farkon Ciroman Kano da ya zama sarki. Sarki Abdullahi Bayero mutum ne mai haƙuri da kuma tattalin jama’arsa.

A zamanin sarki Abdullahi aka kammala aikin ruwan famfo da aka jawo daga Kogin Calawa zuwa Gwauron Dutse sannan aka rarraba shi zuwa unguwanni da gidaje. Sannan kuma a zamaninsa aka kammala aikin wutar lantarki. A zamaninsa aka kammala ginin asibitin Shahuci. Sannan a zamaninsa aka gina makarantar ‘Middle School’ da ta koma Kwalejin Rumfa (Rumfa College) a yau. Wannan makaranta tana nan a kan titin zuwa Jami’ar Bayero daga Gidan Murtala. Tana nan tana kallon katangar badala da ke tsakanin Sabuwar Ƙofa da Ƙofar Ɗanagundi. Sannan a lokcinsa aka gina makarantar koyon sana’o’i ta Ƙofar Nassarawa. Sarki Abdullahi shi ya sa aka yi ta ciccike kududdufan da ke cikin birnin Kano saboda kiwon lafiya. Sannan a lokacinsa aka gina makarantun aikin shari’a da ta koyon aikin shari’ar, wato ‘Judicial’ da kuma ‘Law school’. Ita judicial ita ce ta koma makarantar koyon harshen Larabci wato (School for Arabic Studies) da ke Ƙwalli a halin yanzu.

Sarki Abdullahi Bayero ya mulki Kano na tsawon shekara ishirin da bakwai.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub