Me ka ke nema?


Shafin Farko

Abdullahi Ɗan Dabo 1855 – 1882 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Abdullahi ɗan Dabo shi ne sarki na arba’in da bakwai a jerin sarakunan Kano. Sannan kuma sarki na huɗu a jerin sarakunan Fulani.

A zamanin Sarki Abdullahi Ƙasar Kano ta yi yaƙe-yaƙe da dama. Ta yi galaba wasu lokutan, a wasu loutan kuma a galabce ta.

Sarki Abdullahi ya kawo abubuwan ci gaba a ƙasar Kano da dama. Daga ciki akwai cewa shi ya sake gina Zauren Turakin Manya bayan ya rushe, sannan ya gina Masallacin Turakin Manya. Sannan kuma a zamaninsa aka fara harba bindiga idan sarki zai hau, wanda wannan yana ɗaya daga cikin al’adun masarautar Kano har zuwa yau ɗin nan.

Sarki Abdullahi ɗan Dabo ya yi sarautar Kano tsawon shekara ishirin da bakwai da wata takwas kafin ya rasu a Karofi. Allah ya jiƙansa da rahama. Amin.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub