Me ka ke nema?


Shafin Farko

Babba Zaki Ɗan Yaji 1768 – 1776 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Babba Zaki shi ne sarki na arba’in da ɗaya a jerin sarakunan Kano. Shi kuam sarki ne mai hikima da kuma sanin tarihi. Sannan kuma fasihi mai kula da jama’a.

Sarki Babba Zaki ya yaƙi Auyo a zamanin sarkin Auyo Abubakar har sai da ya kusa shiga cikin garin Auyo. Sannan kuma ya yaƙi Burumburum har sai da ya shiga cikinta. Ƙi-da-so ya zama jama’ar Burumburm suna yi masa yaƙi yana na ko baya nan. A dalilin haka ne ma ake yi masa kirari da “Jan rina gasa giwa”.

A zamanin sarki Babba Zaki a fara aiki da bindiga a dukkan sarakunan Kano. Yana da ɗabi’un da suka yi kama dana Larabawa.

Sarki Babba Zaki ya gina gida a Takai, har saida aka zaci kamar ma zai koma can da zama. Amma daga baya Kanawa suka roƙe shi ya dawo cikin gari. Yana da manya jarumai guda biyar masu ɓarin wuta da suka hada da: Sarkin Sankara Nagarki, Sarkin Bebeji Dambo, Sarkin Majiya Kimfirmi Makaman Baubawa, Sarkin Jarmai Acur, da kuma Sarkin Dawaki Maiza. Sarki Babba Zaki ya mulki Kano tsawon shekara takwas kafin ya mutu.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub