Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bawa Ɗan Muhammadu Kukuna 1660 – 1670 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Bawa shi ne sarki na talatin da biyar a jerin sarakunan Kano. Sarki Bawa mutum ne malami, adali kuma mai nagarta. Ya mulki Kano cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba yaƙi a ciki da wajen Kano. Shi ne sarkin day a gina Goron Fagaci, shi ya sassaƙa Kujera ya ajiye ta a zauren Turakin Manya, shi ya gina Soron Dikko, duka a cikin gidan sarki. A zamaninsa wani makarancin Alƙur’ani malam Abdullahi ya zo Kano. Kuma Allah ya yi masa baiwa da murya saboda haka aka gina masa ɗaki a ƙofar zauren Turakin Manya yana ɗebewa sarki kewa da karatun Alƙur’ani da daddare sannan kuma yana yi amsa wa’azi a cikin watan Ramalan har watan ya ƙare. Bayan mutuwar Ɗan Lawan sarki ya ce da malam Abdullahi “Kai ne Ɗan Lawan”. Sannan kuma ya sa shi cikin masu kiran salla a birnin Kano. Sarki Bawa ya yi sarauta ta tsawon shekara goma da wata huɗu da kwana ishirin.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub