Me ka ke nema?


Shafin Farko

Daɗi Ɗan Bawa (1670 – 1703 Miladiyya)


   Gabatarwa

Sarki Daɗi shi ne sarki na talatin da shida a jerin sarakunan Kano. Sarki Daɗi ya yi nufin ƙara faɗin garin Kano a lokacinsa amma mashawartansa suka ce da shi kar ya yi, kuma ya haƙura. Haka nan sarki Daɗi ya yi nufin fita wajen dan yaƙi da Kwararrafawa a nan ma mashawartansa suka das hi kar ya fita. Yana nan zaune cikin gari wata shekara sai Kwararrafawa suka shigo Kano ta Ƙofar Gadan Ƙaya. Suka dinga sara kashe jama’a har said a suka kai Bakin Ruwa. Da labara ya ishe sarki maza-maza sarki ya ɗaura ɗamarar yaƙi ya tare su a Jakara ya yi ta kisansu har sai da ya fatattake su. Daga nan kuma sai yai wuce Daura ‘yan sauran Kwararrafawan da suka rage suka bishi har sai da suka je Jalli sannan suka juyo.

Haka nan a zamanin sarki Daɗi ne Sarkin Gaya Farin-Dutse ya kangare ya ƙi bada kuɗin haraji har tsawon shekara uku. Daga baya sarki ya hilace shi ya kama shi ya kashe, sannan ya naɗa Sarkin Dawaki Duba a matsayin sarkin Aujara. Sarki Daɗi ya yi sarauta ta tsawon shekara  talatin da uku da wata takwas sannan ya rasu.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub