Shafin Farko

Muhammadu Kisoke 1509 – 1565 Miladiyya


<

Gabatarwa

Sarki Muhammadu shi ne sarki na ishirin da biyu a sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Lamis. Sarki ne mai himma.  A zamaninsa ya yaƙi ƙasar Hausa Gabas da Yamma, Kudu da Arewa kuma ya yi nasara.

Sarki Kisoke ya yi yaƙi da sarkin Borno kuma ya gagari sarkin Borno. Bayan da sarkin Borno ya zo Kano ta gagareshi, sai sarki Kisoke ya sa aka hau kan ganuwa aka dinga yi masa kirari kamar haka: “Kisoke Cirata, Kisoke Borno, Kisoke maganin Ciratawa”.

An samu yawaitar shigowar manyan malamai zuwa Kano. Daga cikin irin waɗannan mashahuran malamai akwai, shehu Batunashe wanda ya kawo Ashafa Kano, sai Ɗangwauron Duma. Sannan kuma akwai Shehu Abdussalami wanda shi kuma ya kawo Mudawana, Jami’u Sangiri, da kuma Samarƙandi; dukkan waɗannan littattafan addini ne. Sannan a wannan zamani ne wani mutum wais hi Tubi ya zo daga zazzau ya yi karatu a hannun Shehu Batunashe.

Sarki Kisoke shi ya gina masallacin Rumawa bayan da Shehu Batunashe ya buƙace da yin haka kuma ya aikata. A zamaninsa ne dai wasu mashahuran malamai biyu wad a ƙani suka zo daga Borno. Sunansu Shehu Kursiki da Shehu Magume. Sarki Kisoke ya nemi ya naɗa Shehu Kursiki a matsayin alƙalin Kano amma sai ya yaƙi. Da sarki ya buƙaci ƙaninsa day a zama shi kuma sai ya yarda. Shehu Magume ya karɓi alƙalancin Kano sannan ya kafa rumfa a ƙofar fada.

Sarki Muhammadu Kisoke ya yi sarautar Kano ta tsawon shekaru hamsin da takwas. Daga nan rai ya yi halinsa.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.