Shafin Farko

Muhammadu Nazaki ɗan Zaki 1618 – 1623 Miladiyya


Gabatarwa

Muhammadu Nazaki Ɗanzaki shi ne sarki na ishirin da takwas a jerin sarakunan Kano. Bayan hawansa kujerar mulki ya aikewa da Sarkin Katsina neman sulhu. Sarkin Katsina yaƙi. Katsinawa suka fito zuwa Kano. Sarki ya tare su a Ƙaraye, ya yaƙe su suka tarwatse. Kanawa suka kwashi ganima suka koma gida.

Da shekara ta juyo, sai Sarki Muhammadu ya sake ɗaura ɗamarar yaƙi ya fita zuwa Kalam. Ya bar Wambai Giwa a gida dan tsaron gari. Da sarki ya fita sai Wambai Giwa ya ce, “Me zan yi wa sarkina domin zuciyarsa ta yi fari?” Sai aka ce das hi, “Ai sai fa ka ƙara wannan alƙarya”. Ya ce, “to”. Ya ƙara ta tun daga Ƙofar Dogo ahr zuwa Ƙofar Gadonƙaya, daga Ƙofar Dukawuya zuwa Ƙofar Kabuga, har zuwa Ƙofar Kansakali. An ce duk ranar da za a yi wannan aiki yakan fito da kaɓakin abinci dubu da shanu hamsin. A saboda haka duk jama’ar gari ke zuwa wannan aiki. Bayan an gama aikin ya zaɓi mutane alfayaini (dubu biyu) ya basu tufafi, ya yanka shanu ɗari uku a Ƙofar Kansakali. Sannan ya bawa malamai sadaka mai yawa.

Bayan dawowar sarki daga yaƙi, ya tarad da wannan aiki da Wambai Giwa ya yi. Sarki ya yi matuƙar farin ciki da wannan ci gaba da aka samu. Saboda haka sai sarki ya ce, “Wane abu zan ba wannan mutum domin in faranta masa zuciyarsa?” Mutane suka ce, “Ai sai ka bas hi gari”. Sai ya bashi Ƙaraye. Wambai Giwa ya tafi Ƙaraye ya yi ta yaƙar Katsinawa, ya tara dukiya mai tarin yawa da dawakai dubu da bayi ɗari. Sarki Muhammadu Nazaki Ɗanzaki ya yi sarautar Kano Tsawon shekaru biyar da wata ɗaya.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.