Shafin Farko

Muhammadu Sanusi 1953 – 1963 Miladiyya



Muhammadu Sanusi I

Gabatarwa

Sarki Muhammadu Sanusi shi ne sarki na 53 a jerin sarakunan Kano, sannan kuma sarki na 11 a jerin sarakunan Fulani.

Sarki Muhammadu Sanusi babban malamin addini ne sannan kuma sufi. Mutum ne maras tsoro, managarci, sannan kuma masananin addini. Da hawansa karagar mulkin Kano ya fara da tsarkake masarautar Kano daga ƙazantar giya, sata, da kuma karuwanci. Sarki Muhammadu Sanusi shi ne sarkin da ya riƙa zartarwa da mashaya giya haddi a sarari, karuwai kuma yana tsare su a gidan kaso, su je su yi idda bayan gama iddarsu sai kuma su yi aure; idan sun samu miji. Samun wannan miji shi ne belin karuwa.

A zamanin sarki Muhammadu Sanusi an ƙara gina wasu makarantu da asibitoci da dai sauran kayan more rayuwa. A lokacinsa aka gina makarantar babbar fimare ta Birnin Kudu 1954, sannan a zamaninsa aka giggina makarantun U.P.E. a wasu unguwannin Kano guda uku da suka haɗa da Jarƙasa, Makafin Dala, da kuma Kurawa a cikin shekarar 1960. Sannan a zamaninsa aka gina makarantar horas da malamai (Kano Teachers College) a shekarar 1957. Sannan kuma a zamaninsa aka gina katafaren asibitn ƙashi na Dala. Da sauran muhimman ayyuka da aka gudanar a zamaninsa.

MaNazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.