Shafin Farko

Muhammadu Sharif  Ɗan Daɗi 1703 – 1731M


Gabatarwa

Sarki Muhammadu shi ne sarki na talatin da bakwai a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Maryam.  Ita kuma ‘ya ce a wajen Sarkin Gaya Farin Dutse. A lokacinsa Gayawa suka samu ɗaukaka.

Sarki Muhammadu shi ne sarkin da ya fara karɓar harajin wata-wata a kasuwar Kurmi. Shi ne sarkin da ya yaƙi Ƙiru. An ce ya tura Wambai Duba ne shi kuma da ya je ya maida Ƙiru toka, ya kwashi ganimar bayi, dawaki, da sauran nau’ukan dukiya. Sannan kuma a lokacin Sarki Muhammadu ne Zamfarawa suka ci Kano da yaƙi. An gwabza wannan yaƙi a ‘Yargaya, Zamfarawa suka fatattaki Kanawa.

Sarki Muhammadu shi ne Sarkin da ya gina birnin Gaya ta hannun sarkin Gaya Janhazo. Shi ne ya gina birnin Takai, Tsakuwa, da Dawaki. Sarki Muhammadu ya mulki Kano tsawon shekara ishirin da takwas da wata goma.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.