Shafin Farko

Shekarau Ɗan Alhaji 1649 – 1651 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Shekarau shi ne sarki na talatin da ɗaya a jerin sarakunan Kano. Sarki shekarau shi ne sarkin day a kawo ƙarshen yaƙi tsakanin ƙasar Kano da ƙasar Katsina ta hanyar sulhu. An saka manyan malamai a gaba kamar irin su Shehu Atuman, malam Bawa da Liman ‘Yandoya. A cikin jawabinsa Shehu Atuman ya ce, “Wanda ya fara kisan wani tsakaninku ba zai sami nasara ba in Allah ya so, har ranar ƙiyama”.  Shima sarautarsa bata yi tsawo ba, ya yi sarautar Kano tsawon shekara ɗaya da wata bakwai da kwana ishirin da huɗu.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.