Shafin Farko

Sarki Warisi Ɗan Bagauda 1063-1095M


Gabatarwa

Warisi, shi ne sarkin Kano na biyu wanda ya gaji mahaifinsa Bagauda. Sunan mahafiyarsa Saju.

Tun barin Bagauda Kano, gari ya ci gaba da bunƙasa ta kowace fuska; ƙaruwar arziƙi, yawan jama’a, faɗaɗar gari da ma kafuwar wasu sabbin yankunan. Saboda haka sai Kanawa suka sake aikewa da wakilansu zuwa gareshi suna masu roƙonsa da ya daure ya ƙaurato zuwa gare su. Amma dai shima kamar mahaifin nasa a Sheme ya yi mulkinsa har ya gama. Amsar da sabon sarki ya baiwa jama’arsa da ke zaune a Kano ita ce cewa, gaskiya shi shekaru sun riga sun cimmasa, saboda haka ba zai samu dawowa nan ba.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.