Shafin Farko

Yakufu ɗan Kisoke 1565 M


Gabatarwa

Yakufu ɗan Kisoke shi ne sarki na ishirin da uku ajerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Tunasa. Sarautarsa bata yi tsawo ba. Ya mulki Kano tsawon watanni huɗu da kwana ishirin. Wani mutum da ake kira Gulle daga cikin zuriyar sarakunan nan Kano ya tuɓe shi. Bayan day a tuɓe shi sai Yakufu ya fice daga cikin garin Kano ya tafi zuwa ga wani malami a ƙauye ya yi ta karatunsa har lokacinsa ya yi. Bayan da Gulle ya tuɓe shi sai Galadima Sarkatunya shi kuma ya yaƙe shi. An ɗauki tsawon kwanaki arba’in ana gwabza wannan yaƙi kafin Galadima ya kashe Gulle.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.