Me ka ke nema?


Shafin Farko

Dawuda Abu-a-Sama Ɗan Yaji 1776 – 1781 Miladiyya


Gabatarwa

Dauwada shi ne sarki na goma sha biyar a jerin sarakunan Kano. Dawuda ƙani ne ga sarki mai murabus. Wato sarki Umaru. Sunan mahaifiyarsa Auta. Ana yi masa laƙabi da ‘Baƙin Damisa’.

A zamanin wannan sarki aka fara cinikin bayi a Kano. A wacan lokaci ba wata kasuwa a cikin birnin Kano. Sai dai su masu bayin sukan zarga musu igiya suna yawo da su kwatankwacin yadda a yanzu masu sayar da raguna kan yi a lokacin sallar layya. Akan gansu suna yawo kwararo-kwararo suna kora ragunansu. Duk mai sha’awa idan suka gifta ta gabansa sai ya tsayar da su  a yi ciniki. To haka suma masu sayar da bayin suka ringa yi. Bambancin kawai shi ne cewa a wancan lokacin idan fataken bayin suka fito daga ƙasashe irin su Katsina, Zazzau, Damagaran, Daura, Hadeja da sauran gurare, sai su samu dillali ɗan gari. Sai su zargawa bayin nan igiya mai ‘yar tazara da juna da ake cewa ‘zarara’. Idan mai sha’awa ya gani sai a daidaita. A wancan lokacin ba kuɗi sai dai sukan yi irin cinikin nan ne da ake cewa ‘ban gishiri in baka manda’. Wato ka bada wani kaya kai ma a baka wani irin kayan daban. To a wancan lokacin akan sayi bayi ne da dawakai, ko kuma wani abu daban. Akan karɓi dawakai uku ko huɗu a madadin bawa ko baiwa ɗaya.

Sannan a lokacinsa ne wani ƙasaitaccen hakimin ya yiwo ƙaura daga Borno zuwa Kano. Wannan hakimi sunansa Dagaci.  Kuma a wannan lokaci ne aka sauyawa Ƙofar  Adama suna zuwa Ƙofar Dagaci saboda shigowar wannan hakimi ta wannan Ƙofa.  An yi wannan a shekarar 1425 Miladiyya.

Bayan shekaru goma sha bakwai Sarki Dauda yana kan gadon mulki, sai Allah ya saukar masa da wani zazzaɓi mai zafi wanda har takai baya iya fitowa. Sarki Dauda ya yi wannan zazzaɓi na tsawo makonni biyu, inda daga ƙarshe ya rasu. Ya rasu yana da shekaru sittin da uku a duniya.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub