Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Giji Masu Ɗanwarisi  1095 – 1134 Miladiyya


Gabatarwa

Gijimasu shi ne Sarkin Kano na uku, ya gaji mahaifinsa Warisi Ɗan Bagauda shi kuma Ɗan Bayajidda. Sunan mahaifiyarsa Yanas.

Da hawan wannan sabon sarki sai kanawa suka yi wuf, suka sake tura buƙatarsu ta ya baro Sheme ya dawo ya zauna tare da su a Kano, kuma Kanon ma a yankin Gazarzawa. A wannan karo Kanawa suka dace haƙa ta cimma ruwa, sarki ya amince. Sai dai, da sarki Gijimasu ya shigo Kano, bai sauka a ko’ina ba sai yankin Dutsen Dala, gurin da cibiyar masu bautar Tsimbirbira suke.


Dutsen Dala.

Saukarsa a wannan wuri ya tayarwa da sauran magadan shugabannin masu bautar Tsimbirbira hankali, inda saida har ta kai ga sun yi taron tattaunawar gaugawa a wajen shugabansu na yankin Jakara wanda suka cimma matsaya akan cewa ba za su yarda ya rushe musu gumkin Tsimbirbira ba matuƙar suna raye.  Saboda su a zatonsu ya zaɓi ya zauna a nan ne dan ya kawo ƙarshen bautar Tsimbirbira.

Da Sarki Gijimasu ya samu labarin wannan tattaunawa ta su, sai ya aike musu da cewa yana mai roƙonsu da su zo su haɗa kai su kafa al’umma ɗaya ƙarƙashin sarautarsa. Su yarda su bishi a matsayin sarki. Jin wannan gayyata sai ya bawa waɗannan mutane mamaki wanda aka ce har sai da shi shugan nasu ya yi yunƙurin aurar da ‘yarsa ga ɗan Sarki Gijimasu amma wani babban galadiman shugaban masu bautar Tsimbrbira ya hana shi. Saboda shi a tasa fahimtar in har haka ta ƙullu to idan tafiya-ta-yi-tafiya su za su koma ba komai ba. Jin wannan ta sa jama’ar Dala suka yarda suka miƙa wuya cikin sauƙi. Wannan kuma shi ne sarki na farko da ya yi nasarar haɗe waɗannan jama’u guda biyu waɗanda suka daɗe suna cin gashin kansu ƙarƙashin inuwa ɗaya, suka zama ƙasa ɗaya, al’umma ɗaya.

Wannan nasara da Sarki Gijimasu ya samu ta haɗe dukkan kewayen Kano ta wanca zamani ya zama abu guda ɗaya, sai kuma ya sake gayyatar waɗannan jama’a ta Dala da cewa su zo su haɗa ƙarfi waje guda su gina ganuwar da zata zagaye garin dan samun kariya da abokan gaba da kuma miyagun dabbobi. Wanda kuma hakan aka yi. Wannan shi ne farkon gini ganuwa da ƙofofi da aka yi a Kano.

An fara wannan gini daga Ƙofar Rariya; wacce gurbinta yana tsakanin Ƙofar Ɗan’agundi da Ƙofar Na’isa. Daga nan gini ya ci gaba zuwa Ƙofar Mazugal, zuwa Ruwa, sannan sai Ƙofar Adama. A kwana a tashi gini yana ci gaba har sai da ya kawo Ƙofar Adama, daga nan ya shige zuwa Ƙofar Gudan. Kama-kama gini ya ci gaba zuwa Ƙofar Waika, daga nan ya zarce zuwa Ƙofar Kansakali, daga nan sai Ƙofar Kawun-gari inda daga ƙarshe ya ƙare a Ƙofar Tuji.

Da Sarki ya samu nasarar yin wannan jan aiki, sai kuma ya ɗora a kan faɗaɗa ƙasa. Inda ya runtuma zuwa kudanci wanda sai da ta kais hi har wajen su Gano. Tarihi ya nuna cewa da masarauta ta faɗaɗa sai Sarki Gijimasu ya fara bada wasu yankuna a kula masa da su. daga cikin guraren day a bayar akwai Gano, wanda aka bawa sarkin Rano ya kula masa da su.

Bayan dogon zamani yana mulki, shima Sarki Gijimasu kamar kowane mai rai sai ya koma ga mahliccinsa.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub