Kofar Na'isa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Dogo/Ƙofar Na’isa, Kano 1470


Gabatarwa

Sarki Muhammadu Rumfa ne ya gina wannan Ƙofa. Asali an gina wannan Ƙofa ce a garin Gwale wacce yanzu ta zama Unguwa a cikin birnin Kano. A Gwale an gina wannan ƙofa a kusa da gidan wani masaƙi mai suna Dogo. Shi wannan masaƙi yana da wata bishiya a ƙofar wannan gida nasa da ya ke zama yana saƙa. Shi mutum ne dogo, a saboda haka mutane suke yi masa kirari da, “Dogo ka fi ƙarfin mari”, shi kuma ya ke amsawa da, “Ko ba gaskiya”. A saboda haka da aka gina wannan ƙofa sai sarki ya naɗa shi sarkin ƙofa kuma aka yi mata suna daga sunansa.

Ana nan sai wata rana wasu Fulani suka zo fadar sarki daga garin Yadakwari, kudu da Kura kaɗan, suka kawo ƙara cewa ɓarayi sun zo sun sace musu shanu. Da sarki ya ji haka sai ya sa aka kira masa ɗansa wanda ya ke ji da shi, mai suna Abubakar Mai Unguwar Munduɓawa. Daga nan sai sarki ya bashi umarni cewa ya yi maza ya haɗa runduna ya fita su bi waɗannan ɓayari ya kamo masa su.

Haka kuwa aka yi. Nan-da-nan Abubakar ya haɗa runduna suka fita ta Ƙofar Kudu (Ƙofar ɗan’agundi). Suka yi ta tafiya har Allah ya kai su wannan gari na Yadakwari. Daga nan suka fara ɗaukar sawun waɗannan ɓarayi suna bi, har sai da suka kai wani ƙauyen Maƙarfi mai suna ɗanguzuri, duk a Ƙasar Zazzau (Zariya). Da waɗannan ɓarayi suka hangi wannan runduna sai suka auka musu. To, ka san an ce sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. Saboda haka wanna ruduna ta Abubakar sai suka faɗa waɗannan ɓarayi da yaƙi sai da suka kashe su tatas. Sannan suka damƙa waɗannan shanu ga waɗannan Fulani, su kuma suka kama hanyar komawa gida.

Da suka iso gida sun yi nufin shiga ta Ƙofar Dogo, amma da Dogo sarkin ƙofa ya hango wannan runduna sai ya yi maza ya rufe wannan ƙofa, zatonsa abokan gaba ne. Suka ƙwanƙwasa masa ya ƙi ya buɗe. Daga baya sai suka ce da shi mu rundunar Mai Unguwar Munduɓawa ne kuma ma muna tare da shi. Saboda haka sai ɗan sarki Abubakar mai Umguwar Munduɓawa ya magantu. Duk da haka dai Dogo ya ce ba zai buɗe ba koma waye.

Daga nan sai Abubakar ɗan Sarki kuma Mai Unguwar Munduɓawa ya kaɗa linzamin dokinsa ya yi Gabas. Bai tsaya ko’ina ba sai gurin da Ƙofar Na’isa take a yanzu. Kusa da wannan guri kuma dama akwai wasu ƙauyuka da suka haɗa da, Sharaɗa, Ja’in, Maidile da kuma Shekar Barde. Saboda haka Abubakar ɗan sarki ya tura wasu daga cikin mutanensa zuwa waɗannan ƙauyuka da ke kusa da wannan ƙofa aka aro masa kayan aiki, kamar irin su fartanya, gatura da sauransu. Sannan ya sake tura wasu daga cikin jama’arsa su je su zagaya su shiga ta Ƙofar Kudu, su gayyato jama’a da kayan aiki. Haka kuwa aka yi, ba jimawa sai ga jama’a ta haɗu da kuma kayan aiki.

Da jama’a suka haɗu sai Abubakar ɗan Sarki ya nuna musu irin aikin da ya ke so su yi masa da kuma yadda za su yi shi. Yana tsaye suka fara haƙe gefen gwalalon nan har sai da ruwan ya tsiyaye, sannan suka shiga gonaki suka haƙo ƙasa suka cike wannan gwalalon har sai da ya haɗe da badala, sannan suka fara huda ƙofa. Da Mai Unguwar Munduɓawa ya ga aiki ya fara kankama sai ya kaɗa linzaminsa zuwa Ƙofar Kudu ya shiga ta nan. Da ya isa gida sai ya turo wasu jama’ar da shanu guda biyar da kuma mata masu girki da kayan abinci. Haka aka yi ta aiki ana cin abinci har tsawon kwanaki shida, sannan aka huda ƙofa. Da aka kammala wannan aiki sai ya sa aka je aka ciro ƙyauren Ƙofar Dogo ta baya sannan aka rufe ƙofar kai kace dama can ba ita.

Faruwar wannan al’amari ta sa Dogo ya je fada ya kai ƙara. Ya kuwa yi dace fada tana zama kuma Abubakar Mai Unguwar Munduɓawa ya nan. Sai ya ce da sarki, ina ƙarar Abubakar Mai Unguwar Munduɓawa ya je ya sa an toshe Ƙofar Dogo an gina masa wata sabuwa. Sai sarki ya tambayi ɗansa Abubakar cewa don me ka sa aka yi haka? Sai shi kuma ya amsa da cewa, “Allah ya bawa sarki nasara “Don na isa”.  Sai sarki ya ce da shi tunda ka ce “Don na isa, sai a riƙa kiran wannan ƙofa da suna Ƙofar Ƙofar Na’isa”.

Manazarta


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub