Kofar Sabuwar Kofa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Rumfa/Sabuwar Ƙofa, Kano (1933)


Gabatarwa

Sarkin Kano Abdullahi Bayero ne ya gina wannan ƙofa da ake kira Ƙofar Rumfa. Sunan ya samo asali ne daga makarantar Midil da yanzu ta koma kwalejin Rumfa (Rumfa College). Shi kuma sunan Rumfa asalin sunan wani sarki ne daga cikin sarakunan Kano, wato Muhammadu Rumfa. An kuma samar da wannan ƙofa ne dan sauƙaƙawa ‘yan makaranta zagayen da suke yi wajen zuwa Makaranta ko dai su fita ta Ƙofar Ɗan’agundi ko kuma ta Ƙofar Nasarawa waɗanda duka sun yi nisa.

Ita wannan ƙofa yanzu an fi saninta da Sabuwar Ƙofa. Tana nan a kan titin zuwa Jami’ar Bayero daga gidan Murtala daga hannunka na dama. Idan aka shiga cikinta zuwa mahaɗa ta ƙarshe, idan aka yi hagu za ta ka mutum zuwa hanyar da za ta kai ka Ƙofar Nasarawa har zuwa gidan gwamnatin jahar Kano, ko kuma idan aka yi hagu zuwa fadar Masarautar Kano.

Manazarta:


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub