Kofar Dawanau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Ɗanƙwai/Ƙofar Dawanau 1112


Gabatarwa

Sarki Gijimasu ne ya gina wannan ƙofa.  An sakawa wannan ƙofa suna daga sunan ɗan Kano Maƙeri na uku. Zamanin sarkin Kano Muhammadu Kisayoke, a cikin shekara ta 1470 Miladiyya aka canja wa wannan ƙofa suna ta koma Ƙofar Danau. Gwangwazo (2003), ya kawo cewa, akwai wani manomi Bamaguje mai suna Dannau ɗan Gunda wanda ke da wata makekkiyar gonar da takai kimanin mil ishirin a kusa da wannan ƙofa. Daga sunansa aka samu wannan suna. An ce shi kansa sarki Muhammadu ya gina wani gidan gona ne a yankin gurin da ya ke zuwa ya huta. Saboda haka sai ya yi umarni a riƙa kiran wannan ƙofa da sunan Ƙofar Dawanau.

Manazarta:


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub