Shafin Farko

Naguji Ɗan Ɗariƙi 1194 – 1247M


Gabatarwa

Wannan shi ne sarki na shida a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Yankuma ko Muntaras. Sarki Naguji ɗa ne ga sarkin Kano Yusa, shi kuma ɗan Sarki Gijimasu, shi kuma ɗan sarkin Kano Warisi, shi kuma ɗan Sarki Bagauda.

Shima ya ci gaba da faɗaɗa masarautarsa kusan ta gefen da mahaifinsa ya mutu ya bari. Ya yaƙi mutane tun daga Kura har zuwa Tsangaya. Daga nan ya ɗora zuwa yaƙin Santolo wanda ya ɗauke shi har tsawon shekara biyu amma abu ya gagara. Dole sarki ya karkata akalar dokinsa zuwa gida saboda barin baya da ƙura da ya yi. Abun kuwa da ya faru shi ne cewa ganin ya ɗauki lokaci bai dawo gida ba, sai dangin Tsimbirbira suka fara yunƙurin yi masa tawaye, saboda haka da isowarsa garinsa sai kawai ya kama manya-manyan cikinsu ya yayyanka. Daga cikin waɗanda ya yanka akwai Samagi Ɗan Mazauda, Doriyi ɗan Bugazau, Burdarganguta ɗan Doron-maje, da kuma Buzuzu ɗan Jandodo. Sauran mabiyansu kuma ya ɗora musu haraji na tumuni (kasha ɗaya cikin takwas) na abinda suka noma. Wannan kuma shi ne asalin fara karɓar haraji a hannun talakawa a ƙasar Kano.   Ya mulki Kano na tsawon shekaru hamsin da biyar sannan ya mutu.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.