Shafin Farko

Shekarau Ɗan Ɗariƙi 1290 – 1307 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Shekarau shi ne sarkin na takwas. Sarkin Kano Shekarau ɗa ne ga sarkin Kano Yusa wanda ake kira Ɗariƙi, shi kuma ɗan sarki Gijimasu, shi kuma ɗan sarkin Kano Warisi, shi kuma ɗan Sarki Bagauda.

Sarkin Kano Shekarau ɗan sarkin Kano Ɗairiƙi ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara goma sha bakwai. Masu bautar Tsimbirbira sun bishi har gida sun yi sulhu da shi. Sarki ne da ya kasance mai son zaman lafiya. Saboda kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsa da masu bautar Tsimbirbira har sai da suka kusan sanar da shi sirrin bautar, amma babbansu Samagi ya ƙi fir! Yana mai cewa in suka yi haka za su koma ba komai ba a mance da ƙabilarsu. Har ya mutu bai yi yaƙi da su ba.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.