Shafin Farko

Tsamiya ɗan Shekarau 1307 – 1343M


gabatarwa

Sarkin Kano Tsamiya shi ne sarki na tara a jerin sarakunan Kano. Shi ɗa ne ga sarkin Kano Shekarau, shi kuma ɗan sarkin Kano Yusa wanda ake kira Ɗariƙi, shi kuma ɗan sarki Gijimasu, shi kuma ɗan sarkin Kano Warisi, shi kuma ɗan Sarki Bagauda. Sunan mahaifiyarsa Sajamta.

Sarki Tsamiya shi ne sarkin da ya fatattaki masu bautar Tsimbirbira. Mutum ne da ya yi fice wajen gwarzantaka, sadaukantaka, kwarjini, gashi kuma da tsananin fushi da ƙarfi. Da hawansa gadon mulki ya sanar da maguzawa cewa “Ana gadon soyayya, haka nan kuma ana gadon ƙiyayya. Ba komai tsakanina da shi sai yaƙi” ya ce da su gaskiya ba zai yaudare su, saboda matsoraci ne ke yaudara. Jin waɗannan maganganu na sarki ya tayar da hankalin maguzawa. Suka koma suka tattaunawa suka cimma matsaya kan cewa su bashi dukiya mai tarin yawa. Daga cikin abubuwan da suka kai masa akwai bayi har ɗari biyu. Amma ya yi fatali da wannan ta yi nasu. A wata ranar Asabar sarki ya aike Marukashi garesu da saƙon cewa su shirya sarki na tafe ranar Alhamis. Ga abin da saƙon ke cewa, “Ranar Alhamis ina zuwa Ƙaguwa in Allah ya so, in shiga cikin gininta, in ga abin da yake cikinsa, in rushe ginin, in ƙone itaciyar”.

Lokacin da maguzawa suka ji faɗar sarki sai hankalinsu ya tashi. Saboda haka duk gunda suke a wannan yanki sai suka riƙa tururuwa zuwa gidin wannan gunki nasu. Suka yi dandazo da kayan yaƙinsu a gurin har zuwa hudowar alfijir na ranar Alhamis. Alfijir na hudowa sarki ya fito da jama’arsa suka nufi gindin gunki. Da sarki ya kai wajen sai suka hana shi shiga. Sai sarki ya waiga ya kira sunan ɗaya daga cikin gagararrun mayaƙansa ya ce, “Ina Bajere?” Yayinda Bajere ya ji haka sai ya fito da mashinsa ya dinga sukar kafirai yana kai su ƙasa. Guri ya hautsi ne, yaƙi ya kai yaƙi, har sai da Bajere ya samu shiga ɗakin da gunkin yake, yana shiga ya tarasa da wani mutum ya jingina a jikin gunkin yana riƙe da wata jar macijiya. Yana sukarsa da mashi sai ya rusa wani ihu wuta tariƙa fita daga bakinsa, hayaƙi ya turnuƙe gari, ya fito daga ɗakin da gudu. Yana fitowa sauran jaruman sarki da ke waje su bi shi da gudu tare da sarki. Sai ya ruga ya yi wajen Ƙofar Ruwa. Can ya je ya faɗa wani kududdufi, sarki ya tsaya bakin gurin har sai da ya kai wani lokaci, da suka gab a fito ba sai suka dawo. Ko kafin su dawo duka sauran jama’ar maguzawa sun gudu sun bar gurin, sai wasu jarumai ‘yankaɗan da suka miƙa wuya. Sarki ya shiga ɗakin gunki, ya ga abin day a gani. Da ya fito ya ce das u, “Me ya hana ku gudu?” suka masa masa da cewa, “Ina zamu gudu?” sai ya ce das u “To, madalla”. Sannan ya ce ku sanar da ni abin da ke cikin gunkinku. Suka sanar da shi. Ya yin da suka sanar das hi sai ya ce da Dunguzu, “Kai ne sarkin Cibiri”. Ya kuma ce da Makare, “Kai ne sarkin Gazarzawa”. Ya ce da Gamazu, “Kai ne sarkin Kurmi”.

A zamanin sarki Shekarau aka fara busa Ƙaho ana yi masa kirari kamar haka:  “Zauna daidai, Kano garinka ce.” Ya yi mulki na tsawon shekaru talatin da bakwai.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.