Shafin Farko

Umaru Ɗan Kanajeji 1410 – 1421M


Gabatarwa

Sarki Umaru shi shi ne sarki na goma sha huɗu a jerin sarakunan Kano. Shi ne Umaru ɗan Ibrahim Kanajeji. Sunan mahaifiyarsa Yatari. Sarki Umaru malami ne mai ƙoƙarin aikata addini. Shi almajiri ne a wajen malam Ɗanƙurudumus. Tun yana ɗanƙarami yake karantar da ilimin fiƙihu. Ya yi mulki na tsawon shekaru goma sha biyu. Iya tsawon mulkinsa ƙasar Kano ta zauna lafiya shiru, ba tashin hankali, ba yaƙe-yaƙe ba zalunci.

Tarihi ya nuna cewa Sarki Umaru ya yi murabus ne daga gadon sarauta sakamakon wa’azi da wani abonkinsa ya yi masa. Sarki Umaru ya kasance yana da wani aboki tun tasowar yarinta. Sunan wannan abokin Sarki malam Abubakar. Wata rana, bayan sarki ya kamala bayar da karatu a gidansa da ke Kabuwaya, sai wannan abokin nasa ya zo ya yi masa sallama ya ce zai fita karatu zuwa gabas (Borno). Suka yi sallama, sarki ya yi masa addu’ar sauka lafiya da kuma dacewa da abin da za a je nema da kuma dukkan kariya. A kwana a tashi, bayan wasu shekaru, wata rana Sarki Umaru yana tsaka da bada karatu kwatsam, sai ga wannan aboki nasa mai suna Abubakar ya dawo. Da isowarsa ya taras ana karatu, ya samu guri ya zauna tare da kiyaye dukkan haƙƙoƙin majalisin karatu. Bayan da aka kamala karatu dukkan almajirai suka waste, sai ya zama daga sarki sai wannan baƙo nasa. Sai malam Abubakar ya yiwa sarki  gargarɗi yana mai cewa das hi, “Ya Umaru, har yanzu kana son matar nan ma’abociyar yaudara, wacce masu hankali suka ƙi aurarta, da sannu ka ciji yatsarka akanta, a lokacin da da-na-sani ba za ta yi akmfani ba”. Sannan ya ci gaba da yi masa gargaɗi, ya tsoratar das hi duniya, ya kuma gargaɗe shi game da lahira.

Bayan wasu ‘yan kwanaki sai sarki ya tara dukkan dogarai, fadawa, da dukkan wani mai ruwa-da-tsaki a fada ya karanta musu wasu baituka na waƙoƙi. Sannan ya sanar das u cewa shi daga yau ya sauka a kan kujerar mulki, zai koma gefe ya ci gaba da karantarwa. Hakan kuwa aka yi, sarki Umaru ya bar kujerar sarautar Kano a cikin shekarar 1421 Miladiyya. Lokacin yana da shekaru arba’in da tara da haihuwa. Bayan shekara bakwai da barinsa gadon mulki Allah ya karɓi abinsa. An binne shi a maƙabartar Wali mai Geza wanda wannan suna ya samo asali ne daga ƙabarinsa kasancewa bayan an binne shi a wannan maƙabarta da damina ta juyo sai geza ta fito ta kewaye kabarinsa. Wannan maƙabarta ita ce maƙabartar Ƙofar Mazugal a yau. Tana nan tana kallon kasuwar shanun Kano (wato kara) wacce ke haɗe da mayanka. Ba nisa Tsakaninta da Tsohon Kamfanin buga Jaridu na ‘Triumph’ daga gabasa, sannan kuma dab take da Ƙofar Mazugal daga Yamma. Ƙarshen katangarta daga yamma mahaɗa ce (wato junction). Idan ka dawo Gabas za ka Taho kasuwar canji kuɗi ta Wafa da ke Fagge. Idan kuma ka yi Yamma za ka shiga Ƙofar Mazugal zuwa Gwammaja. Idan kudu ka ɗauka kuma za ka biyo ta gaban mayanka ka tsallaka zuwa Kasuwar Ƙofar Wambai. Idan kuwa ka yi Arewa za ka wuce ta gaban Filin Dalar Gyaɗa har zuwa Kasuwar Alhazai (Hajj Camp).

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.