Shafin Farko

Usmanu Zamna Gawa 1343 – 1349 M


Gabatarwa

Usmanu shi ne sarki na goma a cikin jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Kumaryaku. Ya samu wannan suna na Zamna Gawa saboda kisan Tsamiya da ya yi, sannan kuma ya kulle ƙofar ya zauna a cikin gida tsawon kwana bakwai. Lokacin day a fito ba a san yadda ya yi da waccar gawa ba. Binne ta ya yi? Cinye ta ya yi? Ba wanda zai iya ɗorar da labari sai shi sai Allah masanin abin da ke ɓoye da na bayyane. Ya mulki Kano na tsawon shekaru bakwai.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.