Shafin Farko

Yaji ɗan Tsamiya 1349 – 1385 M


Gabatarwa

Sarki Yaji shi ne sarki na goma sha ɗaya a jerin sarakunan Kano. Asalin sunansa Ali, saboda zafin zuciya da yake da ita shi ya saka ake kiransa da sarki Yaji. Shi ne ya kori sarkin Rano daga Zamnagaba. Ya zauna a Bono tsawon shekaru biyu. Sannan ya tafi Kura ya zauna tare da Ajawa, Warjawa da Arawa.

A lokacinsa ne Wangarwa suka zo Kano suka Kawo Musulunci.
Sarki Yaji ya karɓi wangarwa hannu biyu-biyu, a hannunsu ya karɓi sallah. Sannan ya gina musu masallaci a wancan gurbin da ya karya gunkin Tsimbirbira (Yankin Dala kenan). An ce sarkin Gazarzawa wanda ɗaya ne daga cikin maguzawan da suka saura, yakan ɗebi jama’arsa kullum da dare su je su yi najasa (kashi) sannan su gogga a jikin masallacin. Ganin haka ta saka sarki ya saka mai gadi amma basu daina ba. Sukan je su yaudare shi. Basu daina wannan mummunan aiki ba har sai da Wangarawa suka yi addu’a Allah ya makantar da su. Bayan makancewarsa aka tuɓe shi daga sarauta (sarkin Gazarzawa) sannan aka yi  masa sarkin makafi. Wannan ita ce farkon sarautar makafi a Kano.

Haka nan sarki ya umarci dukkan jama’ar masarautarsa da sallah kuma suka bi. Bayan wannan sarki Yaji shi ya ci Santolo da yaɓi. Ya roɓi malaman Wangarwa da su masa addu’a ya je ya yaɓi Santolo. A wannan lokacin, Santolo ita ce kaɗai babbar ɓasa da ta rage. Kuma cin ta da yaɓi zai karya lagon duk wani mai bautar gunki. Hakan kuwa aka yi, jama’ar Wangarwa da Kanawa suka haɗu suka tada runduna mai ɓarfi suka ɗunguma zuwa Santolo. A rana ta farko an wuni ana gwabza amma ba wanda ya yi galaba a kan wani. Kashe gari da fudowar alfijir sarki ya ɗaura ɗamarar yaɓi. Suna shiga a wannan rana Allah ya kawo nasara.

Sarki Yaji ya yi sauratar Kano na tsawon shekaru talatin da bakwai. Haɓiɓa ya kawo ci gaba sosai a wannan masarauta ta Kano.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.