Shafin Farko

Yusa Ɗan Gijimasu 1136 – 1194M


Gabatarwa

Sarki Yusa wanda ake kira da Ɗariƙi, shi ne sarki na biyar a jerin sarakunan Kano. Ya hau kan karagar mulkin Kano bayan rasuwar yayyensa. Shi ɗa ne ga sarkin Kano na uku. Wato Sarki Gijimasu, shi kuma ɗan sarkin Kano Warisi, shi kuma ɗan Sarki Bagauda.

Marubuta tarihin Kano sun rinjaya akan cewa shi ne sarkin da ya faɗaɗa Kano ya mai da ta babbar ƙasa. Shi ya ci garuruwa irin su Ƙaraye da yaƙi har sai da ya dangana Kano da ƙasar Katsina da kuma Zariya. Sannan kuma shi ya ɗorawa mabiya Tsimbirbira biyan haraji na tumunin duk abinda suka noma.

A wani lokaci da sarki Yusa ya fita yaƙi dan ƙara girman ƙasa, sai wankin hula ya nemi kai shi dare, har ya ɗauki lokaci mai tsawo bai dawo ba. Garin irin jimawar da ya yi bai dawo gida ba sai waɗancan masu bautar Tsimbirbira suka nemi su yi masa tawaye, da ya dawo sai ya aka yayyanka manyansu daga ciki akwai Shamagi Ɗan Mazauda, da Doriyi ɗan Bugazau. Sarki Yusa yana da mayaƙa gogaggu da suka haɗa da Tuje, Fasau, da Iyagari, da Kamfaragi. Ya yaƙi dukkan garuruwan da ke sashen kudu tun daga Gwarmai har zuwa Farin-ruwa. Yusa ya mulki Kano na tsawo shekaru sittin, sa’an nan ya mutu.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.