Ƙofar Sarki Musa
Wannan suna na wannan ƙofa ya samo asali ne daga shigowar da Sarki Musa ya yi ta wannan ƙofa a lokacin da Turawa suka dawo da shi daga Zangon Daura, da nufin haɗe masarautun da suke cikin wannan masarauta. Wannan ta faru ne a cikin shekarar 1906. An samo wannan labari daga ofishin Wakilin Tarihi na Masarautar Daura a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016.
Manazarta:
Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.
Tattaunawa da Wakilin Tarihin na Daura da kuma Dogarin Sarkin Daura mai suna Ɗandaushe, a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016.