Shafin Farko

Jama'iyyar NEPU


Gabatarwa

Jama’iyyar siyasa ce a jamhuriyyar farko ta siyasar Najeriya. An kafa wannan jama’iyya a birnin Kano wacce a lokacin ita ce helikwatar Lardin Kano (Kano Province); wato kenan tun kafin samun ‘yancin kan Najeriya. Masu kishin Ƙasa ‘yan areawacin Najeriya, su suka kafa wannan jama’iyya.

Cikakken sunanta shi ne Northern Element Progressive Union wanda za a iya bashi ma’ana ta Ƙungiyar ‘Yan Arewa Masu Son ci Gaba. Marigayi Alhaji (Dr) Yusuf Maitama Sule Ɗanmasanin Kano, shi ne ya raɗa mata wannan suna. Kuma, wannan ita ce cikakkiyar jama’iyyar siyasa ta farko a Arewacin Najeriya.

Kafuwa

Tun kafin kafa jama’iyyar NEPU a matsayin jama’iyyar siyasa a cikin shekarar 1950, an fara yi mata shimfiɗa, biyowa bayan abin da ya gudana a babban taron Ƙungiyar Jama’iyyar Mutanen Arewa (JMA) da aka yi a birnin Kano a cikin shekarar 1949. Ita kuma JMA, ƙungiya ce ta raya al’du. A lokacin da aka gudanar da taron, wasu jama’a masu hangen nesa suka fahimci irin maƙarƙashiyar da Turawan mulkin mallaka suka shirya na hana ƙungiyar rikiɗewa ta koma jama’iyyar siyasa. Saboda tsoron da suke da shi na nemawa Najeriya ‘yancin kai kamar yadda ta faru da su a ƙasar Indiya.

Mutane irin su Abdulƙadir Ɗanjaji, Malam Abba Maiƙwaru, Malam Bello Ijumu, Yusufu Maitama Sule, da sauransu, su suka kafa tushen kafa wannan jama’iyya ta NEPU a shirinsu na ko-ta-kwana idan aka samu tangarɗa wajen mayar da ƙungiyar JMA zuwa jama’iyyar siyasa (Yakasai, 2012), wanda kuma daga ƙarshe hakan ce ta faru.

A taron da aka yi a karo na biyu na wannan ƙungiya ta JMA a garin Jos cikin shekarar 1950, a nan aka yanke shawarar cewa, ba za a mayar da wannan ƙungiya ta JMA zuwa jama’iyyar siyasa ba. Wannan kuma ita ce ta sake bayar da damar sake buɗe sabon shafin da aka fara shimfiɗawa tun a Kano na kafa wata sabuwar ƙungiyar da za ta zama cikakkiyar jama’iyyar siyasa, dan ɗorawa daga inda aka tsaya. A wannan gari na Jos, wasu daga cikin waɗancan mutane da aka ambata a sama suka ci gaba da tuntuɓar wasu daga cikin waɗancan mahalarta taro da suke ganin suna da ra’ayi iri guda na kafa jama’iyyar siyasa.

Bayan komawar mahalarta wancan taro garuruwan da suka fito, sai Malam Bello Ijumu; wani Bayerabe mazaunin Kano amma kuma ɗan asalin garin Kabba; wacce a yanzu ta ke cikin jahar Kogi a Arewacin Najeriya, ya ɗauki gabaren kai-komo tsakanin wasu ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙungiyoyin da ya ke ganin za a iya samun daidaiton ra’ayi na a kafa jama’iyyar siyasa.

Daga cikin irin waɗannan ƙungoyoyin akwai Ƙungiyar Matasan Kano (Kano Youth Association), da kuma Ƙungiyar Masu Zumunta (TMZ) ta Fagge. Ɗaiɗaikun mutanen kuwa akwai mutane irin su Abdulƙadir Ɗanjaji, Maitama Sule, Mudi Sipikin, Sani Darma, da kuma Babaliyya Manaja waɗanda suka fito daga Ƙungiyar Matasan Kano. Sai kuma Malam Abba Maiƙwaru da sauransu daga Ƙungiyar Masu Zumunta ta Fagge.

Waɗannan mutane da ƙungiyoyi su ne jigon kafa wannan jama’iyya ta NEPU. “Wani Malam Bello Ijumu, shi ya zo ya same ni ya gaya min abin da yake so. Ni kuma na zayyana masa sunayen mutanen da zai tuntuɓa ba tare da ya sanar da su cewa ina da masaniya ba. Wanda sai daga baya bayan an yi taron mutane takwas a ranar takwas ga watan takwas; taron da ake yiwa laƙabi da taron takwas sannan na ce ya sanar da su cewa ni na bayar da sunayensu. To a irin wannan zuwa da yake yi ne ya gaya min cewa ga sunan da suke so a sakawa wannan jama’iyya. Wato Northern Element Progressive Association (NEPA); wanda suna ne wata rusasshiyar ƙungiyar yaɗa al’adu. Ni kuma na ce da shi a cire Association a mayar da ita Union. Saboda haka sai ta zama Northern Element Progressive Union (NEPU)”. In ji Marigayi Ɗanmasanin Kano a tattaunar da muka yi da shi a ranar 14 ga watan Disamba na shekarar 2016.  Ya ci gaba da cewa, “Saboda a wancan lokacin, Turawa basa son su ji duk wani abu da ya shafi association, saboda abin da ya faru dasu a Indiya”.

Saboda haka Malam Bello Ijumu shi ne ya kafa tubulin gina jama’iyyar NEPU. Marigayi Alhaji (Dr.) Yusuf Maitama Sule kuma ya raɗa mata suna. A ranar wata Alhamis, 8 ga watan 8 na shekarar 1950 (8/8/1950), wasu mutane takwas suka zauna a gidan Malam Bello Ijumu da ke lamba 4, a titin Ibadan (Ibadan Road), da ke cikin unguwar Sabon Garin Kano, suka yarda da kafa wannan jama’iyya tare da amincewa da wannan suna da Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano ya raɗa mata.

Akwai saɓani dangane da jerin sunayen mutanen da suka halarci wannan zama. Yakasai (2012), ya ruwaito Malam Magaji Ɗanbatta wanda shi ya rubuta bayanan da aka tattauna a wajen taron ya ce mutanen sun haɗa da Malam Bello Ijumu, Malam Abba Maiƙwaru, Musa Kaula, Babaliyya Manaja, Mudi Sipikin, Mr. Samuel Jegede, Abduƙadir Ɗanjaji, da kuma shi kansa Malam Magaji Ɗanbatta.

Babban Taro

Bayan samun nasarar kafa jama’iyyar NEPU kamar yadda aka zayyana a sama, sai kuma ta gudanar da babban taronta a Sinimar El-Duniya da ke Kano. An ɗauki kwanaki huɗu ana gudanar da taron daga ranar 3 zuwa 7 na watan Afirilu a cikin shekarar 1951. A wannan babban taro aka zaɓar mata shugabanni. Yanzu haka wannan bigire ya haɗe da Kasuwar Kantin Kwari; shi ne ƙarshen wannan kasuwa daga Gabas, inda ya yi iyaka da Titin Ibrahim Taiwo.

Malam Abba maiƙwaru, shi aka zaɓa a matsayin shugaban wannan jama’iyya na farko. Duk da cewa, Yakasai (2012), ya ruwaito cewa, “A haƙiƙanin gaskiya, Malam Aminu Kano ya halarci taron farko na Jama’iyyar a Kano, bayan ya bar aiki a matsayin shugaban kwalejin gwamnati ta horas da malamai da wasu ‘yan makwanni. Ya shirya fitacciyar waƙar nan ta NEPU mai suna Waƙar ‘Yanci”. Wannan ita ce waƙar:

  1. Ya Ta’ala Jalla Sarkin Rahama,
    Ga mu mun taso da halin azama,
    Taimako na gunka Sarki mai sama,
    Don mu san ‘Yanci da adalcin zama,
    Ya Ta’ala Jalla Ga Nijeriya.
  2. Mun nufato ba mu tsoron wahala,
    Gafara sa duk mutum mai gafala,
    Lokaci yau namu ne ba shagala,
    Za mu sau komai mu jure wahala,
    Za mu sau komai mu jure wahala,
    Ya Ta’ala Jalla ga Nijeriya.
  3. Za mu ture dukiya har rayuka,
    Mu na yau ‘yan mazajen ayyuka,
    Kan tafarki mustaƙimi mun zaka,
    Haggyalan duk masu danne talaka,
    Ya Ta’ala Jalla ga Nijeriya.
  4. Zamani ya juya komai na jiya,
    Mun riga mun ɗauki tutar zuriya,
    Dom nu ceto Ummuna Nijeriya,
    Har mu bar suna a wannan duniya,
    Ya Ta’ala Jalla ga Nijeriya.

Hakanan kuma dai Yakasai (2012), ya ruwaito jawabin haɗin guiwa da Malam Sa’adu Zungur da Malam Aminu Kano suka rubuta kuma suka gabatar a wajen wannan babban taro kamar haka:

  1. Cewa, halin da al’amuran walwala su ke gudana a Arewacin Nijeriya, sakamako ne na mulkin danniya da wasu iyalai da ake kira sarakunan gargajiya suke gudanarwa a bisa tsarin danniya.
  2. Cewa, lura da wannan shugabancin na danniya da rashin mutunta jama’a, da jami’an wannan tsukakkiyar doka da Turawan Mulkin Mallaka suka samar kuma su ke goya wa baya, yau ɗin nan a cikin wannan al’umma ta mu akwai wani ra’ayi mai kishiyantar wannan tsari, wanda ya ke kallon kansa a matsayin mai daidaita tsakanin ɓangaren masu zalunci da kuma talakawan da ake zalunta.
  3. Cewa, wannan zalunci za a iya rusa shi ne ta hanyar curewar talakawa waje guda da kuma kuɓutar da su daga hannayen waɗannan ‘yan tsiraru da suka yi gam-dakatar ɗin zamowa shugabanni, ta hanyar sabunta wannan tsari na danniya da kuma maye gurbinsa da tsarin dimokuraɗiyya wanda talakawa za su jagoranta.
  4. Cewa, wannan fafutikar ‘yanci dole ta zama talakawa ne suka yi abar su da kan su.
  5. Cewa, halin da ake ciki yanzu, jami’an gwamnati da suka haɗa da sojojin tarayya, suna wanzuwa ne kawai dan su tabbatar da damammakin waɗannan ‘yan tsiraru waɗanda kansu kawai suka sani. Dole talakawa su daidaitu a hankalce da kuma a siyasance, dan tunɓuke damar da ke hannun gwamnati a matakin tarayya da kuma gudunmomi, saboda waɗannan jami’ai na gwamnati, ciki kuma har da waɗannan sojoji, su zama an juyar da su daga abubuwan amfanin zalunci zuwa masu taimakawa ‘yanci, da kuma kawar da danniya da mulkin zalunci.
  6. Cewa, dukkan jama’iyyun siyasa, ba komai ba ne sai ƙungiyoyin son kai, saboda haka dole talakawa su yi wa waɗannan jama’iyyu bore.
  7. Ƙunigyar Northern Elements Progressive Union ta Arewacin Nijeriya, ta kasance ita ce kaɗai tilo, jama’iyyar talakawa, ta tsunduma fagen siyasa da ƙudurin rage wulaƙantawar da ko ma wacce jama’iyyar munafukai da mayaudara ke yi wa uwarmu Nijeriya, kuma muna kiran dukkanin ‘ya’yan Arewacin Nijeriya da mu cure ƙarƙashin tutarta, ta yadda za mu gaggauta kawo ƙarshen wannan tsarin na danniya, wanda ya ke ƙwace musu gajiyar wahalarsu, ta yadda talauci zai kauce ya baiwa arziƙi hanya; daidaito; siyasa; ƙunci bauta ya koma walwalar ‘yanci.

Saboda haka dai a taƙaice, jama’iyyar NEPU, ita ce jama’iyyar siyasa ta farko a tarihin siyasar Arewacin Najeriya. Duk da cewa, ba a ruwaito Malam Aminu Kano a cikin jerin mutane takwas ɗin da suka gudanar da taron takwas ba, amma an bayyana shi a cikin jerin sunayen mutanen da suka gudanar da jawabai a wajen babban taron jama’iyar na farko. Sannan kuma an ga cewa, haɗakar wasu ƙungiyoyi da kuma ɗaiɗaikun jama’a su suka kafa wannan jama’iya a cikin shekarar 1950.

Manazarta


Abubakar A. T.  (2001). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello Uniɓersity Press, Zaria-Nigeria.

Muhammad S. da Isma’il A (2003). Tarihin Shehu Shagari. M and I Publishers, Kaduna-Nigeria.

Yakasai T. (2004). Tank Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, ɓolume I. Goɓerment Printers, Kano-Nigeria.

Tattaunawa da Alhaji (Dr.) Yusuf Maitama Sule, a ranar 14 ga watan Disamba na shekarar 2016, a gidansa da ke Titin Dawaki (Dawaki Road), wanda yanzu aka mayar da shi Titin Maitama Sule (Maitama Sule Road), Kano.

Tattaunawa da Alhaji Tank Yakasai, OFR, a ranar 1 ga watan Fabarairu na shekarar 2017.



Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Jama'iyyun Siyasa


Alamomi da Tambari

Shugabannin Ƙasa


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin