Shafin Farko

Jama'iyyar PRP


Gabatarwa

PRP Jama’iyyar siyasa ce a Najeriya. An fara kafa wannan jama’iyya a cikin jamhuriyyar siyasar Najeriya ta biyu a garin Kano. Jama’iyyar ta samu nasarar cin zaɓen manyan jahohin arewacin Najeriya guda biyu daga cikin goma na wancan lokacin (1979). Jahohin Kaduna, wacce daga baya aka cire jahar Katsina daga cikinta, da kuma jahar Kano, wacce ita kuma daga baya aka cire jahar Jigawa daga cikinta, su ne jahohin da jama’iyyar ta PRP ta samu nasarar lashewa.

Marigayi malam Aminu Kano, wanda aka fi sani da limamin canji ko jagoran talakawa, shi ne ya jagoranci kafa jama’iyyar bayan samun saɓani da ya yi da ƙungiyar masu kishin ƙasa (National Movement).

Rugujewar jamhuriyyar siyasar Najeriya ta biyu; wato rushewar jamhuriyya ta biyu a siyasar Najeriya, shi ne abin da ya kawo ƙarshen wannan jama’iyya. Sai dai, tsohon gwamnanta na Kaduna, Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa, ya sake sabunta ta a wannan jamhuriyyar da yanzu ake cikinta a siyasar Najeriya.

Kafuwa

An kafa wannan jama’iyya ta PRP a cikin shekarar 1978 biyowa bayan janye takunkunmin siyasa da gwamnatin sojon tarayyar Najeriya ta yi a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1978, wacce shugaba Obasanjo ke jagoranta a lokacin bayan rasuwar Janar Murtala Ramat Muhammed. Takunkumin da ya ɗauki tsawon shekaru goma sha biyu (15/01/1966 – 1/10/1978).

Ɓaraka da aka samu a cikin haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu kishin ƙasa National Movement, tsakanin wasu daga cikin shugabanninta da kuma malam Aminu Kano a ɗaya ɓangaren, a yunƙurin mayar da ƙungiyar jama’iyyar siyasa shi ne abin da ya kai ga dasa ɗan-ba na kafa jama’iyyar ta PRP. Saboda haka ita wannan jama’iyya ta PRP da ƙafafunta biyu aka haifeta; ba a yi goyon cikinta ba bare a yi renonta har ta yi rarrafe. Ko da ma an yin ta wata fuska, to ba kamar yadda aka saba ba. Saboda haka nema ta samu damar yin tserereniya da yayyenta. Har ma ta iya tserewa wasu daga cikinsu.

Ƙungiyar masu kishin ƙasa National Movement, ƙungiya ce da manyan masu kishin arewacin Najeriya suka kafa ta a lokacin zaman majalisar sake nazarin sabon tsarin mulkin Najeriya wanda aka yi a shekarar 1978 aka kuma tabbatar da shi a shekarar 1979. Akwai wasu mutane da ake ganin su ne ja gaba wajen wannan aiki, Shehu Musa ‘Yar’aduwa, wanda a lokacin shi ne shugaban ma’aikata na Majalisar Ƙoli ta Sojojin Najeriya; Alhaji Adamu Ciroma; Dakta I.D. Ahmad daga Kano; sai kuma Dakta Sule Kumo; Alhaji Abatemi Usman; Farfesa Iya Abubakar da kuma Babagana Kingibe. Waɗannan mutane, sune ƙashin bayan kafa waccar ƙungiya ta National Movement.

Bayan an kafa wannan ƙungiya a zauren majalisar sake nazarin sabon tsarin mulkin Najeriya, sai ya zama mambobinta a matakin farko ‘yan waccar majalisa ne zalla. Amma daga baya sai aka gabatar da ita ga ƙungiyar dattawan arewa Northern Consultative Forum. Marigayi malam Aminu Kano, mamba ne a waccar majalisa ta sake nazarin sabon tsarin mulki, sannan kuma shugaban kwamatin rubuta tsarin mulkin. Ƙari a kan haka kuma, shi mamba ne na wannan ƙungiya ta dattawan arewa. Saboda haka, sai ya bayar da shawara ga dukkan ‘yan siyasar arewa NEPU, NPC, MBC da sauransu da cewa su shiga wannan ƙungiya baki ɗayansu. Ya ƙara da bayanin cewa, waɗanda suka kafa waccar ƙungiya ta kishin ƙasa, ba cikakkun ‘yan siyasa ba ne a wancan lokacin. Saboda haka, idan har ƙungiyar ta zama jama’iyya, to su za su fara cin moriyar abun. Saboda su za su zama shugabannin jama’aiyyar. Ganau ba jiyau ba, Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya ce, “wannan harsashe na malam Aminu Kano, shi ne kuma abin da ya tabbata daga baya”. Shi kuwa Alhaji Salihu Tanko Yakasai, makusancin malam Aminu Kano ne. Kusanci kuma na haƙiƙa. Saboda a wannan lokaci dukkan wasu tarurruka da shi Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya ke halarta, yana zuwa ne a matsayin wakilin malam Aminu Kano da kuma tsohuwar jama’iyyarsu ta NEPU.

Bayan an ɗauki lokaci ana tafiya tare da malam Aminu a wannan ƙungiya, sai kuma wata ɓaraka ta faru dab da za a mayar da wannan ƙungiya jama’iyyar siyasa, tsakanin bai wuce sati biyu.

A cikin irin tarurrukan da ake gudanarwa kafin babban taron da za a mayar da ƙungiyar jama’iyyar siyasa, an yi wani taro na kwamatin tuntuɓa coordinating committee na ƙungiyar. A wannan taro ne aka fara samun babban saɓanin da ya fara dasa ɗan-ba na zargin murƙushe burin yin takarar shugabancin Najeriya da shi malam Aminun ya ke da shi a cikin zuciyarsa. Akwai wasu mutane da dama da suka je wajen wannan taro bisa gayyatar wasu daga cikin jiga-jigan wannan ƙungiya da nufin samun zama mambobinta kafin zamowarta jama’iyyar siyasa. Da waɗannan mutane suka je wannan waje, sai sakataren wannan kwamati mai suna Ibrahim Tahir, ya kaɗa jelar kare ya ce bal! ba wanda zai shiga wannan ƙungiya nan take kuma kai tsaye sai dai ya koma jaharsa ya je ya samu wakilan wannan ƙungiya ya shiga ta hannunsu. Kuma daga cikin waɗannan mutane da suka je akwai waɗanda suke fitattu ne, sanannu, kuma gogaggu a harkar siyasar Najeriya. Saboda haka su a nasu ganin, sun girmi su koma jaha, su shiga wannan ƙungiya ta hannun sababbin yankan rake a siyasa. Daga ciki akwai fitattun mutane irin su Cif Agunsaya daga Legas, wanda daga baya ya zama babban shugaba National Chairman na jama’iyyar GNPP ta Waziri Ibrahim. Wannan mutum kuma, malam Aminu Kano ne ya tura shi ya shiga wannan ƙungiya. Saboda haka sai malam Aminu Kano ya kalli abin a matsayin tozartawa gare shi da kuma mutumin nasa da ya tura.

Faruwar wannan lamari, ya yi matuƙar haifar da koma baya ga ita wannan ƙungiya ta National Moɓement, saboda manyan kifaye ne aka farauto, sai kuma yaron ɗan su ya buɗe bakin koma duk suka zurare suka koma kogi. Saboda haka abu ne mai matuƙar wahala a iya tsamo su dukkansu, wanda kuma hakan ce ta faru. A wannan dalili sai jiga-jigan arewacin Najeria Northern Caucus suka kira taron gaugawa.

An yi wannan taro a otel ɗin Daba da ke Kaduna. A wannan taro ne aka tabbatarwa da Ibrahim Tahir Kuskuren da ya tafka. Bayan an gama da duk abin da za a yi, sai kuma wasu daga cikin mahalarta taron suka ce to akwai dacewar a baiwa malam Aminu Kano wani babban muƙami a wannan ƙungiya kafin zaɓen shugabanni. Saboda haka sai aka ambata cewa, malam Aminu shi zai zama babban jami’in hulɗa da jama’a National Publicity Secretary na wannan tafiya, muƙamin da malam ɗin ya kalle shi a matsayin sake ƙasƙantar da shi a karo na biyu. Saboda idan aka duba irin gudunmawar da ya bayar a jamhuriya ta farko, jama’iyyar da ya yiwa shugabanci NEPU, ita ce ta zama babbar jama’iyyar da ta yi adawa da jama’iyyar su Sardauna NPC.

Masu iya magana sun ce, idan aka ƙi ka da kwana, wani sai ya soka da yini. Saboda haka a daidai lokacin da waɗannan abubuwa ke faruwa, wasu ƙungiyoyi kuma da ɗaidaikun jama’a da suke neman mafaka, sai suka rungumi malam Aminu Kano hannaye biyu-biyu.

Abu na ƙarshe wanda ya tabbatarwa da malam Aminu Kano zargin da ya ke yi, shi ne taron da aka yi a gidan Shagari ana gobe za a gudanar da babban taron mayar da ƙungiyar jama’iyya ba tare da an sanar da shi ba. Saboda haka sai malam Aminu ya janye jikinsa baki ɗaya daga harkokin wannan ƙungiya.
Wannan janye jiki da malam ya yi, ita ce ta bashi cikakkiyar damar haɗa kai da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutanen da ke neman dama, suka kafa ta su jama’iyyar suka kuma yi mata suna People’s Redemption Party; wato PRP a taƙaice, wacce kuma ake yiwa take da PRP Nasara.

An kafa wannan jama’iyya a garin Kano a cikin shekarar 1978, biyowa bayan wani taro da aka yi a gidan Alhaji Musa Iliyasu wanda ke cikin unguwar Gwammaja, a Kano. Taron da aka yiwa laƙabi da taron gidan rami.

Ƙungiyar malaman jami’o’i reshen jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wacce Dr. Yusuf Bala Usman ya jagoranta, da takwararta ta jami’ar Bayero ta Kano, wacce mutane irin su Dakta Ɗandatti Abdulƙadir daga baya kuma Farfesa su ke ciki. Sai kuma sauran jama’ar malam Aminu na tsohuwar jama’iyyarsa ta NEPU, da kuma ɗaiɗaikun mutane irin su Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa wanda daga baya ya zama gwamnan jama’iyyar a jahar Kaduna. Su suka haɗu suka kafa wannan jama’iyya.

Manufofi

Dunƙulalliyar manufar kafa wannan jama’aiyya ta PRP ita ce samawa talaka ‘yanci. Amma a ɗaiɗaiku akwai:

  1. Bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa ta hanyar kafa masana’antu.
  2. Samar da ‘yanci ga bankuna da kamfanonin inshora ta hanyar cire hannayen ‘yan ƙasashen waje.
  3. Bayar da guraben ƙaro ilimi ga ma’aikatan gwamnati da kuma malaman makaranta.
  4. Ɗaukaka ƙungiyar ƙodago ta ƙasa.
  5. Ƙirƙiro sababbin jahohi guda uku.
  6. Baiwa manoma rancen kuɗi naira biliyan ɗaya dan haɓɓaka aikin gona.
  7. Hana biyan jangali da haraji ga talakawa.

Wasu daga cikin waɗannan manufofi gwamnatocin jahohin da wannan jama’iyya ta samu kafawa sun aiwatar da su. Misali, cire jangali da haraji da gwamna Abubakar Rimi ya yi a Kano da kuma ƙarin ƙirƙirar sababbin ƙananan hukumomi da ya yi.

Zaɓe

Bayan da aka buɗe kakar yaƙin neman zaɓe ta wannan jamhuriyya ta biyu, ɗan-haƙin da ka rena… sai ya tsolewa manyan jama’iyyu ido. Musamman ma jama’iyyar NPN wacce ita ta lashe zaɓen shugaban ƙasa, amma har da haka, bata iya murƙushe jama’iyyar ta PRP ba a jahohin Kano da Kaduna.

Rushewa

Tsawon ran wannan jama’iyya ta PRP shi ne tsawon ran jamhuriyyar siyasar Najeriya ta biyu. Wanda kuma hakan ta faru ne bayan sanarwar rushe jamhuriyyar ta biyu da ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1983. Wannan shi ne bayani game da farko da kuma ƙarshen jama’iyyar PRP a jamhuriyya ta biyu.

Manazarta


Abubakar A. T.  (2001). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello Uniɓersity Press, Zaria-Nigeria.

Muhammad S. da Isma’il A (2003). Tarihin Shehu Shagari. M and I Publishers, Kaduna-Nigeria.

Yakasai T. (2004). Tank Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, ɓolume I. Goɓerment Printers, Kano-Nigeria.



Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Jama'iyyun Siyasa


Alamomi da Tambari

Shugabannin Ƙasa


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin