Sarakunan Daura
Gabatarwa
Tun farkon kafuwar ta zuwa yau, Daura ta yi sarakuna sittin (60), tun daga kan Abduldari, mutumin da ya taso daga Gabas ta Tsakiya ya fara kafa ita masarautar ta Daura a wani Dausayi da ake kira ‘Gigiɗo’, kamar yadda ya zo a Littafin Taƙaitaccen Tarihin Daura wanda Fadar Mai Martaba Sarkin Daura ta wallafa. Sai dai, akwai wata matsala babba guda ɗaya ta rashin samu cikakken jerin sunayen sarakunan na Daura tun daga dauri zuwa yau. Saboda ko shi ma wakilin Tarihi malam Mamman Siya Abubakar cewa ya yi. “…Ba mu da cikakken tarihin Daura daga lokacin kafuwar mulki, sai bayan jihadin Shehu Usmanu Ɗan Fodiye da ya auku a farkon ƙarni na sha tara…”.
Saboda haka ga ɗan abin da ya samu dangane da jerin sunayen sarakunan Daura.
Rukunin Sarakunan Farko
- Abduldari
- Kufuru.
- Gino
- Yakumo
- Yakunya
- Walzamu
- Yanbamu
- Gizirgizir
- Innagari
- Daurama
- Gamata
- Shata
- Batatuma
- Sandamata
- Jamatu
- Hamata
- Zama
- Shawa
- Bawo
Rukunin Sarakuna na Biyu, Sarakunan Fulani
- Malam Isiyaku
- Malam Yusufu
- Malam Muhammadu Sani
- Malam Zubairu
- Malam Muhammadu Bello
- Malam Muhammadu Altine
- Malam Muhammadu Mai Gardo
- Buntarawa Sogiji
- Magajiya Murnai
Rukunin Sarakunan Haɓe, Tun daga Masu gudun Hijira har zuwa yau
- Sarkin Gwari Abdu (Abdullahi)
- Sarki Lukudi ɗan Tsoho
- Sarki Nuhu ɗan Lukudi
- Sarki Mamman Sha ɗan Sarkin Gwari Abdu
- Sarki Haruna ɗan Sarki Lukudi
- Sarki Ɗan’aro ɗan Sarkin Gwari Abdu
- Sarki Tafida ɗan Sarki Nuhu
- Sarki Sulaiman ɗan Sarkin Gwari Abdu
- Sarki Yusufu ɗan Sarki Lukudi
- Sarki Tafida ɗan Sarki Nuhu (a Karo na biyu)
- Sarki Musa ɗan Sarki Nuhu
- Sarki Abdurrahman ɗan Sarki Musa
- Sarki Muhammadu Bashar
- Sarki Umar Faruq Umar
Manazarta:
Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Masarautar Daura. Wallafar Masarautar Daura. An buga a Ammani Prints, Kano-Nigeria.