Sarkin Dutse Mamman Maisajen Fama 1702 – 1720
Gabatarwa
Sarki Mamman Mai Sajen Fama shi ne sarkin Dutse na ishirin da uku. Shi mutum ne jarumi wanda ya ƙware wajen yaƙi. Wannan dalilin ne ma ya saka aka yi masa laƙabi da Mai Sajen Fama.
Rubutaccen tarihi ya tabbatar da bunƙasar Masarautar Dutse tun kafin zamowarsa sarki (Sanusi, 2009). Ya zuwa lokacin mulkinsa Dutse na da garuruwa goma sha bakwai da suke killace a cikin ganuwarta wacce ke da ƙofofi goma sha biyu da ake ambatar kowace ɗaya da sunan gari mafi kusa da ita kamar haka:
- Ƙofar Maranjuwa.
- Ƙofar Burtilan.
- Ƙofar Yina.
- Ƙofar Ƙoƙiya.
- Ƙofar Bukka.
- Galamawa.
- Ƙofar Ma’ai.
- Ƙofar Tago.
- Ƙofar Kachi.
- Ƙofar Gadadin.
- Ƙofar Galadimawa.
- Ƙofar Rariya.
Duk da cewa waɗannan Ƙofofi sun ɓace, amma har yanzu akan samu sauran abin da ba a rasa ba na daga ɓuraguzan wasu daga ciki. Sarki Mamman Mai Sajen Fama ya rasu a Fagen Fama a lokacin da yake tallafawa Kano dan ta yaƙi Zamfara a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Ɗan Daɗi (1703 – 1731).
Manazarta:
NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.
Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.
Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.
Sarakunan Dutse
Haɓawa
- Tuwai
- Ƙetare
- Tasau
- Maido
- Maigiji-Tandu
- A Maranje
- Babilu
- Labun
- Yakwabu
- Sambore
- Dunhu
- Akuli
- Mantau
- Jawandu-Dogo
- Yusufu
- Mamman
- Yakubu
- Inuwa
- Habu
- Audu
- Mani6
- Hassan
- Mamman
- Yahai
- Ada
- Zubairu
- Mamman
- Amadu
Fulani
- Salihu
- Musa Ahmadu
- Bello
- Suleman
- Ibrahim
- Abdulƙadir
- Salihu
- Ibrahim
- Abdulƙadir
- Abduƙadir
- Haladu
- Halilu
- Hamidan
- Abdullahi
- Bello
- Suleman
- Abdullahi
- Muhammadu
- Nuhu M.S.
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin