Shafin Farko

Kiwon Kifi


Gabatarwa

Wannan kalma ta ‘fishery’ tana da mabanbantan ma’anoni. Oxford Dictionary (2000), Encarta Dictionary (2009), Merriam-Webster Dictionary (2015), sun kalle ta a matsayin ‘guri ko muhallin da ake kamun kifi’. Saboda haka za mu iya cewa kenan wannan kalma ta ‘fishery’ da farko tana nufin wani yanki, ko guri ko muhalli wanda ka iya zama wani yanki na teku, kogi, ko tafki wanda kifi ke rayuwa a gurin kuma gurin ya zama gurin kamun kifi. Kenan, duk wani yanki na kogi ko teku da makamantansu da kifi baya rayuwa a gurin ba za a iya kiransa ‘fishery’ ba.

Sannan kuma tana da ma’ana ta kamfanin da ke kamawa ko sayar da kifi. Wannan kamfani zai iya kasancewa babba ko ƙarami. Duba (Encarta Dictionary, 2009; Oxford Dictionary, 2000; Wikipedia, 2015).

Har-wa-yau dai kuma tana da ma’ana ta dukkan wani abu da ya shafi sana’ar kifi tun daga kiwon kifi, kamun kifi, gyaran kifi, da kuma sayar da kifin, da ma gurare da masa’antun da ake aiwatar da wannan sana’ar. Kai, har ma da dabaru ko hanyoyin kamun kifin sun shigo ciki. Waɗanda suka haɗu a kan haka sun haɗa da (Encarta Dictionary, 2009; Wikipedia 2015).

Sannan kuma akwai 'Fishery', a matsayin fannin karatu da ake koyarwa a fannin aikin gona, wato ‘Agriculture’ da yake koyar da dukkan wani abu da ya shafi harkar kifi kamawa tun daga sanin shi kifin a kan-kansa, kiwata shi, kama shi, gyaggyara shi, sayar da da shi da sauran dangoginsa.

Wannan fanni na aikin gona (fishery), yana bada muhimmiyar gudunmawa wajen samar da ayyukan yi, inganta harkar samar da abinci, da kuma haɓɓaka hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga ga ɗaiɗaikun mutane, masana’antu da kuma ƙasashe a duniya.

Kamun Kifi

Manazarta:


Geunther L. (2016). All About Fish. An ciri daga: http://www.kidzone.ws/animals/fish1.htm

The Daily Climate. (2014). Explosion of gill lice besets Wisconsin's beloved fish. An ciro daga: http://www.dailyclimate.org/tdc newsroom/2014/11/gill-lice

Understanding Evolution. (2016). University of California Museum of Paleontology. An ciro daga: http://evolution.berkeley.edu/

Salmonids. (2016). Salmonids in the Classroom: Salmon Dissection. An ciro daga: http://www.pskf.ca/sd/

Wikiwand. (2016). Fish Fins. An ciro daga: http://www.wikiwand.com/en/Fish_fin The Scottish Government (2015). Types of Fishery. An ciro daga: http://www.gov.scot
/Topics/marine/Salmon-Trout-Coarse/eels/types

Food and Agriculture Organization of the United Nations. (2016). Fisheries Technology. An ciro daga: http://www.fao.org/fishery/technology/en

Aikin Gona



Ɗakin Karatu

Harshen Turanci


Alƙur'ani


Jama'iyyar PRP
Jama'iyyar NEPU
Jama'iyyar NPN


Abinci
Abinci...
Rabe-Rabe
Bitamin
Hanta


Kwamfuta
Amfanin Kwamfuta
Siffofin Kwamfuta
HTML
Algorizim
Ofareshin Risac


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin