Shafin Farko

Siffofin Kwamfuta


Gabatarwa

Siffa a nan na nufin abin da a Turance ake kira characteristics.Saboda yawan da kwamfutoci ke da su a yau, sai ya zama ana yawan samu bambance-bambance game da abin da ya shafi siffofin nasu. Amma ga wasu kaɗan da kusan baka rasa kwamfuta da wasu daga cikin su:

  1. Sauri (Speed): Kwamfuta na da saurin sarrafa bayanai, a yau akwai kwamfutar da ke sarrafa umurni 1,000,000,000,000,000 (miliyan dubu miliyan, daidai da 1015; kwadiriliyan biyu da rabi kenan) ko a ce 1,000,000,000,000,000,000,000,000 (miliyan miliyan miliyan miliyan ɗaya 1024 a dogon lissafi) a cikin sakan ɗaya.
  2. Girman Rumbu (Large Storage): Kwamfuta na da girman rumbun da ke bata damar adana bayanai masu tarin yawa, a yau an samu kwamfutar da ke da rumbun da zai iya ɗaukar bayanai sama da bayit tiriliyan dubu sau 24 (1000Terabyte Ɗ 24); wato kimanin harrufa tiriliyan dubu sau 24.

  3. Rumbun Kwamfuta (Hard Disk)

  4. Raushi (Versatility): Shi ne damar da kwamfuta ke da ita ta yin ayyuka mabambanta masu tarin yawa. Misali, ana iya amfani da kwamfuta ɗaya wajen zane-zanen kalanda, tsara kiɗa da waƙa, gyaran waya, adana bayanai a asibiti, shirya fim, d.s. gwargwadon softwayar da aka ɗura mata. Sai dai wannan siffar ta fi ga Makiro-kwamfuta.
  5. Cif-da-cif (Accuracy): Shi ne damar da kwamfuta ke da ita ta yin aiki kwabo-da-kwabo; wato duk irin aikin da aka saka ta za ta yi kamar yadda abin yake.
  6. Otimatir (Automation): Shi ne damar da kwamfuta ke da ita ta yin aiki ba tare da sa hannun ɗan’adam ba. Kwamfuta na yin ayyukan da ya kamata mutum ya yi ba tare da mutum ɗin ya saka hannunsa ba. 

Manazarta:


Tsangarwa A.M. (2010). Kwamfuta a Sauƙaƙe, Sabon Bugu. Tsangarwa ICT Limited, Kano-Nigeria.