Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Alhaji Ibrahim Dasuƙi, shi ne sarkin Musulmi na 18 a jerin sarakunan Musulunci na Daular Shehu Usmanu Ɗanfodiye. Sannan kuma shi ne na farko a zuriyar Muhammadu Buhari ɗan Shehu Mujaddadi.

Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi mutum ne gogagge a fannin sarauta, mulki, da kuma kasuwanci. Ya yi aikin gwamnati a matakai da yawa kuma na zamani mai tsawo. Ya fara aiki tun kafin samun 'yancin kan Najeriya tare da Hukumar Gargajiya har zuwa Matakin tarayya. Ya yi aiki na tsawon shekaru 45 (1943 - 1988) a matakai daban-daban. Ya kuma yi sarauta ta tsawon shekaru takwas.

Mutum ne shi mai son zaman lafiya; yana da hazaƙa da kuma basira, kamar yadda VOA (2016), su ka hakaito Magajin Garin Sakkwato yana bayyanawa. Ya rasu yana da shekaru 93 (1923 - 2016).


Ƙofar Fadar Masarautar Sakkwato. Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi ya mayar da ita haka

Haihuwa

An haifi Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi a ranar 31 ga watan Disamba na shekar 1923 a garin Dogon Daji. Shi ɗa ne ga Halliru ɗan Barau; sarkin Yamma, hakimin Dogon Daji.

Karatu

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Ibrahim Dasuƙi, ya fara karatun Al-Ƙur'ani tun yana ɗan shekara biyar; 1928. Ya kuma halarci makarantar Elimantare ta garin Dogon Daji a shekarar 1931. Sai kuma ya zarce zuwa makarantar Midil ta Sakkwato a shekara 1935. Daga nan sai Kwalejin Barewa da ke Zariya, makarantar da ya kammala a shekarar 1943.

Gogayyar Aiki

 1. 1943 - 1945, kilak a baitil malin Hukumar Gargajiya ta Sakkwato.
 2. 1953, Ma'aikaci a kamfanin Gaskiya, Kaduna. Kamfanin da ke wallafa jaridar gwamnatin Arewa mai suna Gaskiya ta fi Kwabo.
 3. 1953 - 1954, ‘executive officer’ a gwamnatin Arewa.
 4. 1954 - 1957, Sakataren Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello.
 5. 1957 - 1960, Muƙaddashin sakataren majalisar zartarwa (deputy secretary to the regional government) yanki.
 6. 1958 - 1959, Jami'in hukumar jin daɗin alhazai a Jidda.
 7. 1960 - 1961, Ma'aikacin ofishin jakadancin Najeriya a Khartum, Sudan.
 8. 1961, Rasdan na Lardin Jos.
 9. 1965 - 1967, Sakataren din-din-din (permanent secretary) a ma'aikatar ƙanan hukumomi daga nana kuma ya koma ma'aikatar cinikayya (ministry for commerce).
 10. 1967 - 1989, Ciyaman BCCI, Najeriya.
 11. 1984, Shugaban kwamitin sabunta tsarin gudanarwar ƙananan hukumomin Najeriya.
 12. 1988, mamba a majalisar tsarin mulki.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Adeseun A. (2016). The Burial Of Former Sultan Of Sokoto, Alhaji Ibrahim DasukiDasuki. An ciro a shekarar 2017., daga shafi: http://www.nigerianmonitor.com/alhaji-ibrahim-dasuki-burieddasuki-father-burialphotos/

Amodu T. (2016). Life and times of Sultan Ibrahim Dasuki. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: http://sunnewsonline.com/life-and-times-of-sultan-ibrahim-dasuki/

BBC Hausa (2016). Tarihin Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: http://www.bbc.com/hausa/37964588

Daily Trust (2016). Late 18th Sultan of Sokoto, Ibrahim Dasuki
buried in Sokoto. An ciro a shekarar 2017, daga shafi.: https://www.dailytrust.com.ng/news/general/late-18th-sultan-of-sokoto-ibrahim-dasuki-buried-in-sokoto/171816.htmlya

Garba s. (2016). Allah Ya Yiwa Tsohon Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki Rasuwa. An ciro a shekara 2017. Daga shafin: https://www.ɓoahausa.com/a/allah-ya-yiwa-tsohon-sarkin-musulmi-ibrahim-dasuki-rasuwa/3596292.html

Guardian (2016). Alhaji Ibrahim Dasuki (1923-2016). An ciro a shekarar 2017, daga shafi: https://m.guardian.ng/opinion/alhaji-ibrahim-dasuki-1923-2016/

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Wikipedia (2017). Ibrsjim Dasuƙi. An ciro a shekar 2017, daga shafin https://en.m.wikipedia.org/wiki/Ibrahim_Dasuki


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub