Kunu (Kunun Tsamiya)

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kunu


Gabatarwa

Abinci ne da ake samarwa daga gero. Yana ɗauke da sinadaran da ke taimaka wa jiki ya yi ƙwari.

Ire-Iren Kunu

Akwai nau’ukan kunu da Bashaushe yake yi a Ƙasar Hausa da dama. A wannan rubutun za mu magantu a kan:

 1. Kunun Tsamiya.
 2. Kunun Kanwa.
 3. Kunun Gyaɗa.
 4. Kunun Nono.
 5. Kunun Zaƙi.

Kunun Tsamiya

Sunan wannan kunu ya samo asali ne daga tsamiyar da ake jiƙawa a yi kunun da ita.

Kayan haɗi

 1. Gero.
 2. Tsamiya.
 3. Kayan Ƙamshi (Kananfari, masoro da sauransu).
Matakin Farko
 1. Za a surfa gero, a tankaɗe shi a ware dusa sannan a wanke shi a daka ko a niƙa.

 2. Dusar Gero

 3. Sai a tankaɗe niƙaƙƙen garin gero a fitar da tsaki.

 4. Tsakin Gero

 5. A jiƙa tsamiya ta jiƙu a cikin mazubi mai tsafta.

 6. Ruwan Tsamiya

 7. Sai a ɗebi garin kaɗan a jiƙa shi da ruwan sanyi tsararo abin da ake kira ruwan sirki.

 8. Ruwan Sirki

 9. Sannan a sake ɗiban wani gari a dama shi da kauri a cura gaya (Ida ana buƙata).

 10. Curin Gaya

 11. Sai kuma a ɗebi wani garin gwargwadon buƙata a dama ƙullin kunu da ruwan tsamiya.

 12. Garin Kunu


  Ƙullin Kunu

Mataki na Biyu
 1. A ɗora ruwa a kan wuta. Idan ya fara yin ɗumi sai a jefa gayan nan su tafasa tare har gayan ya dahu (Yana kama da curin ɗanwake).

 2. Dafaffen Gayan Kunu

 3. Sai a kawo tafasasshen ruwan nan a zuba a kan ƙullin kunu da aka dama sannan a rufe shi a mazubi mai kyau a bashi lokaci kaɗan ya haɗa jikinsa.
 4. Daga nan sai a kawo wancan ruwan sirki ana zubawa ana gaurayawa har kunun nan ya haɗu tsaf.


Damammen Kunun Tsamiya

Ya damu da gaya kunun tsamiya, sama gaya ƙasa gaya kunun tsamiya.

Kunun Gyaɗa

Kayan haɗi
 1. Gero.
 2. Ɓararriyar Gyaɗa.
 3. Tsamiya.
 4. Kayan Ƙamshi (Kanafari, masoro da sauransu).
Matakin Farko
 1. Za a surfa gero, a tankaɗe shi a ware dusa sannan a wanke a daka ko a niƙa.
 2. Sai a tankaɗe shi a ware tsaki da kuma gari mai lashi adana garin a mazubi mai kyau.
 3. A soya gyaɗa farar suya a murje ta a bushe sannan a markaɗa ta ko a daka sannan a adana ta a mazubi mai kyau.

 4. Soyayyiyar Gyaɗar Kunu

 5. Sai a zuba gayaɗar can a cikin ruwa idan dakawa aka yi, idan kuma markaɗe ce to dama da ruwanta ake markaɗa ta sannan a tace. A ware butaci daban ruwan kuma a adana shi a mazubi mai kyau.
 6. A jiƙa tsamiya a cikin mazubi mai kyau.
 7. A ɗebi garin gero a dama gaya.
Mataki na Biyu
 1. A tafasa ruwan gyaɗar can da aka tace, tafasa uku.

 2. Soyayyiyar Gyaɗar Kunu Tana Tafasa a Kan Wuta

 3. Idan ruwan ya fara yin ɗumi, sai a zuba gaya a ciki su tafasa tare.
 4. A dama garin kunu da ruwan tsamiya.
 5. A jiƙa wani garin na sirki da ruwan tsamiya.
 6. Idan ruwa ya tafasa sai a sauke a zuba shi a cikin damammen ƙullin kunu sannan a rufe shi a jira kaɗan.
 7. A buɗe rufaffen gaurayen ƙullin kunu da tafasasshiyar gyaɗa sannan a kawo ruwan sirki a riƙa zubawa ana gaurayawa.

Idan har aiki ya yi daidai, za a ga kunu yana sheƙi sannan kuma ƙamshi yana tashi.

Kunun Kanwa

Kayan haɗi
 1. Gero.
 2. Kanwa.
 3. Kayan Ƙamshi (Kanafari, masoro da sauransu).
Matakin farko
 1. A surfa gero sannan a bushe shi a cire dusa a wanke a daka ko a niƙa.
 2. A gyara kanwa ta hanyar ciccire bunu da kuma tsakowawin da ke cikinta sannan a jiƙa.

 3. Ruwan Kanwa

 4. A ɗebi garin gero a dama a cura gaya.
Mataki na Biyu
 1. A ɗora ruwa ya tafasa.
 2. Idan ruwa ya fara ɗumi sai a jefa gaya a ciki su tafasa tare.
 3. A dama ƙullin kunu da ruwan kanwa.
 4. A sauke tafasasshen ruwa a kwara a kan ƙullin kunu sannan a rufe na wasu ‘yan mintuna da basu wuce biyu ba zuwa uku kai har ma biyar ya danganta da yawan kunun.
 5. A buɗe kunu a gauraya har sai ya haɗa jikinsa.

 6. Kunun Kanwa

Kunun Nono

Kayan haɗi
 1. Gero.
 2. Nono.
 3. Kayan Ƙamshi (Ida nana buƙata)
Matakin Farko
 1. A surfa gero, a tankaɗe sannan a wanke a daka ko a niƙa.
 2. A dama ƙullin kunu da ruwan sanyi.
 3. A cura gayan kunu.
 4. A zuba nono a cikin mazubi mai kyau a adana.


Nono

Mataki na Biyu
 1. A ɗora ruwa ya tafasa.
 2. A jefa gaya a ciki su tafasa tare.
 3. A sauke tafasasshen ruwa a kurma a saman ƙullin kunu sannan a rufe zuwa lokaci kaɗan.

 4. Dafaffen Kunu

 5. A buɗe haɗin kunu a riƙa zuba nono ana juyawa har su haɗa jikinsu.


Haɗaɗɗen Kunun Nono

Koko

Kayan haɗi
 1. Gero.
 2. Kayan ƙamshi.
Matakin farko
 1. A rairaye gero sannan a wanke ba tare da an surfa ba.
 2. A jiƙa wannan gero ya samu awanni 24 a ruwa. An fi so a jiƙa shi bayan sallar La’asar. Misali, daga 5:00 na yamma zuwa ta 5:00 ɗin yammar gobe.
Mataki na Biyu
 1. A fitar da gero daga cikin ruwan da ya kwana a wanke.
 2. A zuba kayan ƙamshi a ciki a markaɗa.

 3. Gero da Kayan Yaji

 4. A tace markaɗaɗɗen gero a fitar da butaci sannan a zuba shi a mazubi mai kyau a rufe shi zuwa safiya.

 5. Butacin Gero

Mataki na Uku
 1. A tace garin gero da ya kwana a ruwa domin a samu gasara.

 2. Kwanannen Ruwan Tsari Kafin a Tace


  Ana Tace Ruwan Tsari Domin a Samu Gasarar Koko

 3. A zubar da ruwan tsari (Ruwan da geron ya kwana a cikinsa).

 4. Zallar Ruwan Tsarin Koko

 5. A ɗebi gasarar da ake da buƙata a dama ta a wani mazubin na daban a adana. Idan kuma tana da kauri sosai, sai a zuva ruwa a ɗan tsinka ta kaɗan.

 6. Gasarar Koko

 7. A sake ɗibar wata gasar mai ɗan kauri a dama gaya da ita.
 8. A dama ruwan sirki. Gasara ce ake dama ta tsararo da ruwan sanyi.
Mataki na Huɗu
 1. A ɗora ruwa a tukunya ya tafasa.
 2. A zuba gaya a cikin ruwa idan ya fara ɗumi su tafasa tare.
 3. A sauke tafasasshen ruwa a zuba a cikin damammiyar gasarar koko sannan a rufe a jira na ɗan ƙaramin lokaci.
 4. A buɗe koko a riƙa zuba ruwan sirki ana gaurayawa har su haɗe jikinsu.


Kammalallen Koko

Mataki na Biyar

Idan gasara ta saura sai a sake zuba mata sabon ruwa a adana zuwa gobe.

Kunun Zaƙi

Kayan haɗi

Gero da kayan ƙamshi da sukari

Yadda ake yi
 1. A surfa gero a wanke fes.
 2. A zuɓa kayan ƙamshi a cikin gero a markaɗa.
 3. A tace butacin gero daga cikin markaɗe.
 4. Sai a kawo ruwa a zuba bakin gwargwado.
 5. A zuba sukari gwargwadon baƙata.

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub