Danwake (Ɗanwake)

Me ka ke nema?


Shafin Farko

ƊanwakeTabbas ni ne ɗanwake. Yanzu za ku sha bayani game da ni


Gabatarwa

Ɗanwake, Abinci ne a Ƙasar Hausa, yana daga cikin daɗaɗɗun abincin gargajiyar Hausawa wanda danganta shi da wata ƙasa ko wata ƙabila yake da wahala. Kenan, ɗanwake Bahaushen abinci ne. E mana, gurasar nan ta Kano ai Balarabiya ce sai dai, tsawon zamaninta a garin na Kano ya mayar da ita Bahaushiya. Ana kyautata zaton cewa gurasa za ta haura shekaru ɗari shida a Kano. Shi kuwa, kana faɗin sunansa “Ɗanwake”, to an san abincin Bahaushe ne.

Ɗanwake, abinci ne mai matuƙar gina jiki. Saboda muhimman sinadaran gina jiki da kayan haɗinsa suka tattaro. Kai, a taƙaice ma dai, yana ɗauke da dukkan muhimman sinadarai guda 5 da kowane abinci komai kyawun fatarsa da ƙamshinsa da laushinsa da… yake buƙata kafin ya amsa sunan abinci mai gina jiki. Tirƙashi! Mummuna da aiki kenan. Ɗanwake! A basu mamaki.

Zamowar ɗanwake abincin da ya amsa sunan abinci mai gina jiki, wannan kuma ta bashi damar bayar da gudunmawa mai gwaɓi a fannin kiwon lafiyar ɗan’adam. Ɗanwake, yana bai wa jikin ɗan’adam kariya daga kamuwa da wasu muggan cututtukan da za a iya kiran su rai kwakwai mutu kwakwai ko kuma kabari kusa kamar irin su hawan jini, shanyewar ɓarin jiki, bugun zuciya da sauransu.

A wannan rubutu zan gaya maka kayan haɗin ɗanwake, sinadaran gina jiki da ɗanwake yake ɗauke da su, amfanin ɗanwake wajen kiwon lafiyar jiki, yadda za ka haɗa ɗanwake ka dafa kayanka ka tsame. Yadda za ka ci kuma, wannan ba sai na faɗa ba.

Kayan haɗi

Muhimman kayan haɗin ɗanwaken gargajiyar Bahaushe su ne:

 1. Wake.

 2. Farin Wake

 3. Dawa.

 4. Dawa

 5. Busasshen rogo.

 6. Busasshiyar Rogo

 7. Garin ganyen kuka ko busasshen ganyen kuka.
 8. Kanwa.
 9. Man gyaɗa.
 10. Dakakken barkono (Jan barkono).

To waɗannan su ne muhimman kayan haɗin ɗanwaken Bahaushe. E mana, kasan akwai ɗanwaken fulawa (Hahahaaa…), to ai kasan fulawa sai a hankali. Sannan kuma akwai ɗanwaken alkama. Ita ma alkama Balarabiya ce.

Sinadaran Gina Jiki

Tun da farko na gaya maka cewa, shi ɗanwake yana da muhimman sinadaran da abinci yake buƙata ya zama abinci mai gina jiki. To shi nasa ma har da ƙari. Dukkan waɗancan kayan haɗi da na ambata maka a sama, suna da keɓantattun sinadaran da suke ƙunshe da su.

 1. Wake: Ana samun furotin a jikin wake, duk da cewa, masana sun ce waken suya ne kawai yake bayar da cikakken sinadari furotin, saboda sun gano cewa, yana ɗauke da muhimman sinadarai tara da sai sun samu sannan furotin ya cika. Sauran na’ukan wake kuma suka ce, idan aka haɗa su da hatsi suma suna bayar da cikakken furotin ɗin. Kasantuwar hatsi shima yana ɗauke da wani adadin na sinadarin furotin to idan ya haɗu da wake sai furotin ɗin ya cika cif.
 2. Dawa da Rogo: Suna bayar da cikakken sinadarin kabo-haidiret.
 3. Kuka: Bitamin ce.
 4. Kanwa da Barkono: Suna bayar da sinadarin mineral.
 5. Mansamu gyaɗa: Maiƙo ne (Fat).

Yanzu kenan ka samu furotin, bitamin, kabohaidiret, minarals da kuma maiƙo. To menene ya saura a cikin sinadaran abinci mai gina jiki? Babu. Ya cika tsaf! Ɗanwake kenan.

Bayan waɗannan muhimman sinadarai kuma guda biyar yana ɗauke da ƙarin sinadaran zinc, ayon, faiba, da sauransu. Wannan fa shi ne mai kyauta da ƙari.

Na tabbata ko ban ce da kai komai ba, ka san daga ganin kura za ta ci akuya. Kenan ka san ɗanwake zai taimaka wa jiki sosai. Bari mu shiga taskar gudunmawar da yake bai wa jiki wajen kare shi daga kamuwa da cututtuka da kuma ƙara masa lafiya.

Amfanin Ɗanwake Wajen Kiwon Lafiyar Jiki

Duk wanda ya ci ɗanwake, ana sa ran cewa, jikinsa zai samu fa’idantuwa da waɗannan amfanoni da ma ƙarin wasu:

 1. Kariya daga cutar sikari (Diabetes).
 2. Kariya daga kamuwa da cutar kansa.
 3. Kariya daga kamuwa da cutar ƙiba; wato yin ƙiba maras misali abar da ake kira obesity a Turance.
 4. Gyara fatar jiki ta riƙa sheƙi (Aikin maiƙo kenan).
 5. Ƙara kyawun gashin jiki.
 6. Ƙara wa jiki ƙarfi da kuzari (Ka ji aikin rogo da dawa).
 7. Ƙara ƙwarin ƙashi.
 8. Kariya daga cututtukan zuciya kamar irin su bugun zuciya da saruansu.
 9. Kariya daga kamuwa da cutar hawan jini. Kasantuwar wake da kuka suna ɗauke da sinadaran da ke saukar da gudun jini tare kuma da daidaita sidaran sikari da gulukos da ke cikin jini.
 10. Kariya daga kamuwa da cutar shanyewar ɓarin jiki.
 11. Magance matsalar narkewar abinci; abin da ke haifar da rikicewar ciki.
 12. Ƙarin jini ta hanyar ƙara samuwar jan sinadarin jini (Red blood cells).
 13. Tallafa wa mai juna biyu: Wasu daga cikin kayan haɗin ɗanwake suna ɗauke da sinadarin folik asid (Folic acid), wanda shi ne sinadarin da mace mai ciki take buƙata a farkon watannin ɗaukar ciki domin ƙara girman mahaifa da sauran su. Musamman wake da kuka, duk suna ɗauke da waɗannan sinadari sosai.
 14. Ƙara ƙarfin gani da daddare.
 15. Ƙara ƙarfin garkuwar jiki.
 16. Rage ƙarfin tarin fuka da tarin shiƙa.
 17. Hutasar da gajiya; akwai sinadaran da ke bai wa jiki hutu sosai a ciki.
 18. Maganin cizon ƙwari; cin ɗanwake zai hana gubar da cizon ƙwari kamar irin su sauro suke yi wa mutum yin tasiri a jikinsa.
 19. Kariya daga kamuwa da cututtukan ƙoda.
 20. Narkar da tsakuwar ƙoda (Appendices).

Sai kuma ka faɗaɗa bincike a kan haka. Na tabbata za ka samu ƙari.

Yadda Ake Yin Ɗanwake

Akwai matakai uku da ake bi wajen yin ɗanwake:
Matakin Farko: Harhaɗa kayan ɗanwake

 1. Za a gyara dukkan waɗancan kayan haɗi da na ambata a sama su zama masu tsafta sannan kuma kuɓutattu daga datti.
 2. Sannan a samu mazubai masu kyau a tanada.
 3. Sai a jiƙa garin kanwa a mazubi mai tsafta a rufe.

 4. Ruwan Kanwa

 5. Sai a haɗa wake, dawa da busasshen rogo a mazubi ɗaya. Idan kukar da za a yi amfani da ita ba gari bace, to itama sai a zuba ta a ciki.

 6. Gaurayen kayan ɗanwake

 7. Sai a niƙa waɗannan kayayyaki da aka ambata a sama su zama gari.

 8. Garin ɗanwake a haɗe da garin kuka

Ka ga yanzu kenan ka samu garin ɗanwake. Idan kuma kana son haɗaɗɗe to

Mataki na biyu: Kwaɓi, wannan shi ne haɗa ƙullin ɗanwake
Kwaɓi shi ne gauraya garin ɗanwake da ruwan kanwa. Idan aka gauraya garin da ruwa, to yanzu kuma sunansa ƙulli. Kenan, ƙullin ɗanwake shi ne kwaɓaɓɓen garin ɗanwake. Ga yadda ake kwaɓa ƙullin ɗanwake:

 1. A ɗora tukunya da ruwa gwargwadon buƙata a kan wuta domin ruwan ya tafasa kafin a gama kwaɓa ƙullin ɗanwake.
 2. A zuba niƙaƙƙen garin a mazubi mai tsafta.
 3. Sai a kwaɓa shi da ruwan kanwa.


Ƙullin ɗanwake

Mataki na uku: Jifa, jifan ɗanwake kai tsaye shi ne dafa ɗanwake. Amma, jifa a nan yana nufin saka ƙullin ɗanwake a cikin tafasasshen ruwa domin ya dahu.

 1. A ɗora tunkuya da ruwa a cikinta a kan wuta a bar ruwan ya tafasa.
 2. Jifa: Sai a riƙa gutsuro ƙullin ɗanwake ana jefawa a cikin tunkunya.

 3. Idan aka gutsuro ƙullin sai a tsoma ko a jefa shi cikin tafasasshen ruwa


  Jifan ɗanwake


  Jifan ɗanwake

 4. Bayan an gama jefa ɗanwake tsaf, sai a bashi lokaci kamar mintuna uku zuwa biyar, ya danganta da yawan ɗanwake, girman tukunya da kuma ƙarfin wutar da ake amfani da ita. Amma a sauƙaƙe idan ɗanwake ya yi tafasa uku to ya dahu sai a sauke.

 5. Ɗanwake tafasar farko

Gane Dahuwar Ɗanwake

Idan aka jefa ɗanwake a cikin tafasasshen ruwa za a ga ya nutse ƙasa. Idan ya dahu zai hauro sama. Idan aka tsame shi aka zuba a cikin ruwan sanyi zai yi ƙasa. Waɗannan su ne alamomin tabbatuwar dahuwar ɗanwake.


Ɗanwake dafaffe a ƙasan ruwa

Bayan tukunyar ɗanwake ta tafasa sau uku, za a ga ɗanwaken ya taso sama. Sai a tsamo ɗanwake guda ɗaya a jefa shi cikin wani mazubi mai ɗauke da ruwan sanyi. Idan har ya dahu, to cikin ‘yan daƙiƙoƙi zai nutse ya yi ƙasan ruwan.

Sannu da aiki. E mana, to an gama dafa ɗanwake tsaf ya dahu. Yanzu kuma sai a kawo dakakken barkono da man gyaɗa a kwarara a sama.

Sai dai, ana iya ƙara dukkan abubuwan da ake so, kamar irin su maggi, gishiri, albasa, kifi, man shanu da sauransu.

Tabbasa wannan shi ne bagargajiyen ɗanwaken Ƙasar Hausa.


Ɗanwake da mai da yaji

Da mai da yaji, Ɗanwake da mai da yaji Ɗanwake.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub