Gudunmawar Shafukan Sada Zumunta...

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gudunmawar Shafukan Sada Zumunta


Abubakar Muhammad Tsangarwa
tsangarwa@yahoo.com
+234 803 964 8244


Tsakure

Wannan muƙala (takarda), mai taken Gudunmawar Shafukan Sada Zumunta Wajen Yaɗa Al’adun Hausa a Tsakanin Ɗaliban Kwalejojin Jahar Kano, wacce aka gabatar a babban taron ƙasa-da-ƙasa da Ma’aikatar Adana Kayan Tarihi ta Burkina Faso, tare da haɗin Guiwar Ƙungiyar Makaranta suka shirya, wanda aka yi wa take da Taron Al’adun Hausawa Na Duniya Na Ƙasar Burkina Faso, ta binciko irin amfanin da ɗalibai suka fi yi da shafukan sada zumunta dan tantace cewar, ko suna amfani da su wajen yaɗa al’adun Hausa. Sannan kuma ta fitar da shafin da aka fi amfani da shi wajen sadarwa a tsakanin ɗalibai, ta kuma bada shawarar yin amfani da mafiya shahara cikin shafukan wajen yaɗa al’adun Hausa. An gudanar da wannan nazari a kwalejojin Jahar Kano da suka haɗa da Kwalejin Nazarin Harkokin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano (Aminu Kano College of Legal and Islamic Studies), Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Kwalejin Koyon Aikin Gona ta Audu Baƙo (Audu Baƙo College of Agric), Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (College of Art, Science and Remedial Studies), da kuma Kwalejin Nazarin Harkokin Karkara da Muhalli (College of Rural and Enviromental Studies). An yi amfani da salon tuntuɓar ra’ayi na mai rabo ka ɗauka (Stratified Random Sampling Technique) wajen zaɓar zakarun gwajin dafin gudanar da nazarin. Wannan nazari ya samar da amsoshi ga tuhumomi guda uku da suka haɗa da; wanne shafin sada zumunta aka fi amfani da shi a tsakanin ɗalibai? Menene kyakkyawan alfanun shafukan sada zumunta? Da kuma wanne shafin sada zumunta ne mafi dacewa a yi amfani da shi wajen yaɗa al’adun Hausa?

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub