Kwalejin Katsina

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kwalejin Horas da Malamai ta Katsina


Kwalejin Horas da Malamai ta Katsina

Wannan makaranta mai tsohon tarihi, ita ce makaranta mafi daɗewa a duk faɗin Arewancin Najeriya. Tana daga cikin jagaban makarantun da suka yaye ɗaliban da suka jagoranci Najeriya tun dauri. Daga cikin tsofaffin ɗalibanta akwai Sir Ahmadu Bello, da kuma Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa.

An samar da wannan makaranta a shekarar 1921, sannan kuma aka ƙaddamar da ita a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 1922 ƙarƙashin babban gwamnan Najeriya (Governor General of Nigeria) Sir Hugh Clifford da ɗaliban da yawansu yakai 50 daga dukkan lardodin Arewa (Kangiwa, 2014) na wancan lokacin wanda yanzu ya haɗa dukkan jahohin Arewa guda 19.

Bayan wasu shekaru ana gudanar da karatu a wannan makaranta sai aka canja mata suna ta koma Katsina Higher College a shekarar 1929 (Nigerian wiki, 2003; Barewa Old Boys Association, 2015).

Daga baya an ɗauke wannan makaranta daga wannan gari na Katsina aka mai da ita Kaduna aka kuma canja mata suna ta koma Kaduna College (Nigerian wiki, 2003; Barewa Old Boys Association, 2015). Bayan nan kuma sai aka sake ɗauke ta daga garin na Kaduna aka maida ita garin Zariya, inda aka sake canza mata suna ta koma Zaria Secondary School, sai kuma aka sake canja mata suna ta koma Government College Zaria, sannan aka sake mai da ita Barewa College, sunan da take riƙe da shi har zuwa yau ɗinnan (2016).

Waccan tsohon gini na Kwalejin Horas da Malamai da ke Katsina shi kuma an ayyana shi ya zama gidan tarihi na ƙasa a shekarar 1959. Har ya zuwa yau ɗin nan (2016), wannan makaranta tana nan a garin Katsina.


Mashigar Makaranta

Wani Sashen Wajen Makaranta

Wani Sashen Wajen Makaranta

Ƙofar Sashen Ajujuwa

Ajujuwa

Cikin Aji

Ƙofar Shiga ɗakunan kwana

Manazarta:


Barewa Old Boys Association (2015). Brief History of Barewa College, Zaria. An ciro a shekarar (2016) daga shafin: http://www.boba.org.ng/history.html

Kangiwa M.M. (2014). A short Historical Guide on Katsina National Monuments and Sites.

Katsina Emirate Council (2009). Katsina Emirate Council, Home of Heritage and Hospitality. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: http://www.katsinaemirate.org/

Nigerian Wiki (2008). Barewa Collage. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: http://nigerianwiki.com/wiki/Barewa_College


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub