Katsina Kofar Guga

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Guga, Katsina


Gabatarwa

Wannan ƙofa tana daga cikin ƙofofin da aka gina a ƙarni na 15. Wannan suna nata ya samo asali ne daga sunan wata matar sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo, wacce ta zo ta fallasa asirin shi Bawa Jan Gwarzo na shirin da ya ke yi na kawowa Katsina yaƙi. To da ta zo shiga garin Katsina ta shigo ne ta wannan ƙofa. Saboda jin daɗin wannan labari da ta zo da shi, sai sarkin Katsina na wannan lokacin ya sa aka sakawa wannan ƙofa sunan wannan mata ta Bawan jan Gwarzo (Mamman, 2015).

Amma a Ingawa (2006), ya zo cewa sunnan wannan ƙofa ya samo asali ne daga sunan wani basarake wai shi ‘Buga’, wanda kuma ya fito ne daga zuriyar Durɓawa, wato sarakunan Durɓi. Kamar yadda ya kawo ya ce  shi ne sarkin da ya fara sarautar garin na Bugaje.

Manazarta:


Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.

Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsina

Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub