Muhammadu Korau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muhammadu Korau


Gabatarwa

Sarkin Katsina Muhammadu Korau, shi ne sarki na shida a jerin sarakunan Katsina. Shi Sarki Muhammadu Korau Haɓe ne kuma Musulmi. Ya zo a ruwayar Ingawa (2006), cewa shi Sarki Muhammadu Korau ɗan asalin garin Tsafe (Chafe) ne wacce ke cikin Jahar Sakkwato ta yau. Sarki Muhammadu Korau ya hau gadon sarautar Katsina bayan da ya kayar da sarki Sanau a kokawar da suka buga.

A zamanin sarki Korau ne aka gina masallacin juma’a na farko a garin Katsina, wanda shi wannan masallaci daga baya ya bunƙasa ya koma wata babbar jami’ar karantar da addinin Musulunci. A cikin wannan masallaci akwai wata hasumiya mai tsawo wacce ake yiwa laƙabi da Hasumiyar Gobarau.

Manazarta:


Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.

Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsina

Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub