Kokawar Sarki Sanau da Korau, Katsina

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kokawar Sanau da Muhammadu Korau


Gabatarwa

Akwai ruwayoyi guda biyu dangane da wannan kokawa ta Sarki Sanau da kuma Sarki Korau. Ta farkon wacce muka samu daga gidan mai garin Durɓi ta Kusheyi ta hanya isar da saƙon nan ta Kunne ya Girmi kaka, ta labarta mana cewa shi Korau lokacin da ya zo garin Katsina yana zaune sai ya riƙa yiwa matar sarki Sanau alheri, wato yana kyautata mata har sai da ya samu karɓuwa a wajenta ya kai matakin da duk abin da ya nema idan tana da shi za ta iya bashi. Daga ƙarshe sai ya roƙe ta sanin sirrin ƙarfin kokawar sarki Sanau, sai ta sanar da shi cewa yana amfani da wata laya. Bayan wani ɗan lokaci sai ya sake roƙar ta cewa ta bashi wannan laya ta sarki Sanau yana da wata kokawa. Ta ɗan jinjina kafin ta bashi, amma dai daga ƙarshe ta bashi. Da ya karɓi wannan laya sai ya kuma nemi Sarki Sanau da ya zo su buga kokawa, sarki sanau ya yi shela a gari ya kuma saka ranar kokawa, da rana ta zo Sanau ya waiwaici layarsa ya nema ya rasa, ya tambayi matarsa ta ce masa bata san ina ya ajiye ba. Da aka buga kokawa sai Korau ya buga Sanau da ƙasa. Wannan kaye shi ya kawo ƙarshen sarautar Sanau kuma farkon Sarautar Korau.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub