Ƙofar Ƙwaya, Katsina
Gabatarwa
Ƙofar Ƙwaya ƙofa ce da ke kan hanyar zuwa Dutsinma. Ta samu wannan suna nata ne daga sunan wani mai unguwa da ke zaune a unguwar da wannan ƙofa take. Sunan wannan mai unguwa shi ne ‘Magaji Ƙwaya’; Magaji Ƙwaya mutum ne jarumi (Ingawa, 2006). Amma a ruwayar Mamman (2015) ya kawo cewa sunan wannan ƙofa ya samo asali ne daga sunan wani basaraken Haɓe wanda ke mulkin wani gari mai suna Ƙwaya. Sannan kuma shi wannan basarake shi ke samowa sarkin wannan zamanin nasa hatsi, wato dawa da gero da sauransu. Sannan kuma ya ƙara da cewa wannan ƙofa ta ita ne wani waliyi mai suna Wali Joɗa ya fita garin Katsina lokacin da sarki ya kore shi.
Manazarta:
Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.
Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsina
Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.
Sarakunan Katsina
Haɓawa:
Fulani:
- Tarihin Katsina
- Gidan Korau
- Hasumiyar Gobarau
- Sanau da Korau
- Kwalejin Katsina
- Durɓi ta Kusheyi
- Hukumar Gargajiya
Ƙofofin Katsina
- Ƙofar Guga
- Ƙofar ‘Yanɗaka
- Ƙofar Ƙaura
- Ƙofar Durɓi
- Ƙofar Sauri
- Ƙofar Turmi
- Ƙofar Keke
- Ƙofar Angulu
- Ƙofar Gazobi
- Ƙofar Ƙwaya
- Ƙofar Waziri
- Ƙofar Soro
- Ƙofar Marusa
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin