Katsina Kofar Daka

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar 'Yan Ɗaka, Katsina


Gabatarwa

Ƙofa ce da aka gina tun cikin ƙarni na 15 (Mamman, 2015). Ta samu wannan suna ne daga sunan basaraken da ke riƙe da sarautar ‘Yanɗakan Katsina (Mamman, 2015; Ingawa, 2006). Ita kuma wannan sarauta ta ‘Yanɗaka ita ce sarautar Dutsinma, wato hakimin Dutsinma shi ne ‘Yanɗakan Katsina. A wani zamani can baya a wannan unguwa gidansa yake, saboda haka ake kiran ƙofar da wannan suna. Amma Mamman (2015), ya bambanta a nan da cewa shi basarake mai wannan suna ‘Yanɗakan Katsina yana fita ta wannan ƙofa ne idan zai tafi ƙasarsa haka nan ma kuma idan ya dawo ta wannan ƙofa yake shigowa gari.

Manazarta:


Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.

Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsina

Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub