Katsina Hasumiyar Gobarau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hasumiyar GobarauKatsina


Gabatarwa

Wannan hasumiya mai tsohon tarihi an gina ta a shekarar 1348, a zamanin sarkin Katsina Muhammadu Korau (Kangiwa, 2014). Ita wannan hasumiya wani ɓangare ce ta babban masallacin Juma’a da ke cikin tsohon birnin Katsina. Wannan masallaci ya taɓa zama babbar jami’ar da take a matsayin reshen jami’ar Sankore da ke Timbuktu ta ƙasar Mali. Ko siffar wannan hasumiya na tabbatar da haka. Bayan wannan kuma wannan masallaci shi ne masallacin farko da aka fara yi a garin na Katsina.


Hasumiyar Gobarau, Katsina

Ita wannan hasumiya a wancan lokaci ita ce gini mafi tsawo a garin na Katsina, saboda haka takan zama wata kafa ta leƙen asirin tsaro. Abin nufi shi ne cewa ana hawa kanta a hango nesa, musamman yankin Gobir, dan hango abokan gaba daga nesa idan sun yi nufi kawowa Katsina hari, wannan kuma takan bawa ita Katsina cikakkiyar damar shirya faɗa da waɗannan abokan gaba.


Wani Sashen Garin Katsina daga Hasumiyar Gobarau

Wannan gini da ake gani ba wai shi ne asalin ginin na farko ba, a'a, akwai wani lokaci a baya da gini ya ruguje, a saboda haka a zamanin wani sarki daga cikin sarakunan Katsina sai aka tattara magina na gargarjiya suka sake gina ta da zallar kwaɓaɓɓiyar ƙasa da sauran sinadaran gini na asali.

Manazarta:


Kangiwa M.M. (2014). A short Historical Guide on Katsina National Monuments and Sites.

Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub