Kofar Durbi Katsina

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kofar Durbi Katsina


Gabatarwa

Ƙofa ce da aka gina ta a ƙarni na 15 (Mamman, 2015). Ko kuma ƙarni na 14 a zamanin sarkin Katsina Muhammadu Korau (Ingawa, 2006). Sunan wannan ƙofa ya samo asali ne daga sunan sarautar garin Durɓi wacce yanzu ake kira da Durɓi ta Kusheyi. Ingawa (2006) ya kawo cewa a zamanin da ya shuɗe, sararakunan baya; wanda muƙaminsu ya ke da daidai da na hakiman yanzu, sukan zauna ne a cikin gari, sannan kuma akan kira dukkan unguwannin da suke zaune ciki da sunan sarautarsu, to shi sarkin Durɓi yana zaune ne a wannan unguwa ta kusa da wannan ƙofa, saboda haka sai ake kiranta da sunan wannan hakimi na Durɓi. Mamman (2015) ya kawo wani ra'ayi da ya yi kama da wannan.

Manazarta:


Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.

Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsina

Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub