Alhaji Usman Nagogo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Usman NagogoAlhaji Usman Nagogo


Sarki Nagogo a Fada

Gabatarwa

Sarki Usman Nagogo shi ne sarkin Katsina na arba’in da takwas a jerin sarakunan Katsina, sannan kuma sarki na tara a jerin sarakunan Fulani, kuma sarki na biyu a zuriyar Sulluɓawa.

Usman Nagogo ɗa ne ga sarki Muhammad Dikko. Sunan mahaifiyarsa Hafsatu ko Hansatu a Hausance. Sannan kuma shi ne mahaifin sarkin Katsina na goma a jerin sarakunan Fulani wato sarki Muhammad Kabir Usman. Haka nan kuma shi ne mahaifin gwamnan Lardin Arewa na farko, Manjo Hassan Usman Katsina.

Karatu

Sarki Usman na Gwaggo, ya fara karatunsa tun yana ƙarami a hannun mashahurin malamin nan malam Attahiru wanda ke zaune a unguwar Gambarwa.

A Shekarar 1921 ya fara karatunsa na ‘Elementary’ a makarantar ‘Katsina Provincial School’, karatun da bai kai ga kammalawa ba ya tafi Ingila tare da mahaifinsa. Daga baya a shekarar 1923 ya kammala karatun.

Gogayyar Aiki

Tun kafin zamowar Usman Nagogo sarki, sai da ya riƙe muƙamin shugaban ‘yansada na hukumar gargajiya (NA) a shekarar 1929, kafin daga baya a yi masa naɗin Magajin Garin Katsina Hakimin Birni da Kewaye a cikin shekarar 1937.

Haka nan bayan zamowarsa sarki, an yiwa Usman Nagogo muƙamin ‘Federal Minister of the Colony’, muƙamin da Sarkin Ingila King George VI ya yi masa a ranar 12 ga watan Janairun shekarar 1946. Haka nan sarki Usman Nagogo ya riƙe muƙamin Ministan Yanki (Regional Minister) tun daga shekarar 1955 har zuwa lokacin juyin mulkin 1966.

Sannan ya riƙe muƙamin shugaban Jama’atun Nasir Islam (JNI). Haka nan kuma an yi masa muƙamin shugaban din-din na ƙungiyar ƙwallon Dawaki ta Nigeria (Life President of the Nigerian Polo Association)

Zamowarsa Sarki

Sarki Usman Nagogo ya zamo sarkin Katsina a ranar 19 ga watan Mayun shekarar 1944, naɗin da Arthur Richards, gwamnan Lardin Arewacin Najeriya (Governor of Northern Nigeria) ya yi masa. Wannan naɗi shi ya mayar da shi magajin mahaifinsa Muhammadu Dikko, sannan kuma sarkin Katsina na 48, kuma na 9 a Jerin sarakunan Fulani sannan kuma na biyu a zuriyar Sulluɓawa.

Gudunmawar da ya Bayar

Sarki Usman Nagogo ya bada gagarumar gudunmawa wajen kawo ci gaba a wannan masarauta ta Katsina. Yana daga cikin irin gudunmawar da ya bayar ta bunƙasa ofishinsa na shugaban ‘yansadan hukumar gargajiya (NA) lokacin da yake riƙe da ita ta hanyar faɗaɗa gine-ginen ma’aikatar da kuma ɗaukar sabbin ma’aikata da ya yi.

Rasuwarsa

Sarkin Katsina Alhaji Usman Nagogo ya rasu a cikin shekarar 1981. Ya yi sarauta tsawon shekaru 38, daga 1944 zuwa 1982 A.D.

Manazarta:


Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.

Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsina

Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Univeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.

Wikipedia (2016). Usman Nagogo. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Usman_Nagogo


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub