Sarkin Zazzau Abdulkarim

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Abdulkarim Bakatsine 1834 – 1846 A.D.


Gabatarwa

Malam Abdulkarim Bakatsine shi ne abokin karatun Malam Musa Bamalli. Shi ne sarkin Zazzau na 63, sannan kuma na uku a jerin sarakunan Fulani. Zaɓensa ya biyo bayan rashin daidaituwar al’amura da aka samu tsakanin gidajen sarautar Zazzau guda biyu, wato Mallawa da Barebari. Lamarin da ya gagari masu zaɓen sarki sasantawa ƙarƙashi jagoranci Galadiman Zazzau da kuma sauran jama’a da suka haɗa da Limamin Juma’a da kuma Dokaje. A saboda haka sai suka tuwara Wazirin Sokoto cewa suna bada shawarar naɗin Malam Abdulkarim Bakatsine.

Shawarar tasu ta samu amincewar Wazirin Sakkwato, a saboda haka sai shi Malam Abdulkarim Bakatsine ya zama sarkin Zazzau na 64 sannan kuma na huɗu a jerin sarakunan Fulani.

Shi Malam Abdulkarim Bakatsine Bafulatanin Katsina ne, jikan Malam Sambo ne. Tare suka yi karatu da Malam Musa Bamalli, sannan kuma yana zaune a Zariya tsawon shekara 17 kafin Jihadin Shehu Ɗanfodiye.

Malam Abdulkarim Bakatsine mutum ne masani kuma mai tsananin riƙo da addini wanda hakan ta saka ake yi masa laƙabi da Waliyyi. Tun kafin zamowarsa sarki shi ne Sa’in Zazzau wanda Malam Musa Bamalli ya naɗa, ayyukansa a wancan lokacin sun haɗa da kulada Fulani makiyaya.

Malam Abdulkarim Bakatsine shi ne ya gina babban masallacin Juma’a na birnin Zaria. Ya yi sarautar Zazzau ta tsawon shekara goma sha biyu. Ya rasu a shekarar 1846 A.D.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Northern Nigeria Ministry of Information (1965). The Fascinating Provinces of Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria-Nigeria.

Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London: Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub