Ɓarawon Keke

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muƙyaƙyata: Ɓarawon Keke


A can zamani baya; lokacin da ake bayar da lasisin tuƙa keke a Najeriya, an taɓa yin wani ɓarawa da ya je wani asibiti daga cikin asibitocin wani babban birni daga cikin biranen Najeriya, ya saci keken wani bawan Allah. To a kan keken nan akwai wani kwali ɗaure a kan kariya.

Da ɓarwaon keken nan ya fita wajen asibiti zai gudu da keken nan, sai kiciɓis, ya haɗu da ‘yan sanda masu kamen lasisi; suka riƙe shi, kafin su kai ga yi masa magana, sai ɗaya daga cikin ‘yan sandan ya buɗe kwalin nan, yana buɓewa, sai ya ga gawar jariri a cikin kwali. Sai ɗan sandan nan ya ce da abokan aikinsa, ai wannan ɓarawon yara ne ma ba ɓarawon keke ba. Da ɓarawon nan ya ji haka, sai ya yi tsalle ya ce: “Wallahi a haka na sato keke nan yanzu a asibitin waje kaza, sai ya ambata sunan asibitin”. Ya ci gaba da rantse-rantse cewa, lallai shi ma sato keken nan ya yi a haka, shi ba ɓarawon jarirai ba ne.

Ana tsaka da wannan taƙaddama, sai ga wani dattijo ya zo wucewa a cikin kiya-kiya. Ana zuwa daidai gurin nan, sai dattijon nan ya tsinkayi kekensa, nan-da-nan sai ya buƙaci direba da ya tsaya. Ya ce: “Ga kekena can da aka sace min yanzun nan na hango shi”. Da zuwan dattijon nan gurin ‘yan sanda sai ya wuce gurin keken nasa kai tsaye, sannan ya ce da ‘yan sanda wannan keken nasa ne yanzu aka sace masa shi a cikin asibiti.

Da ɓarawon nan ya ji haka, sai ya ƙara tabbatar da cewa sato keken nan ya yi kuma a asibitin. Sai ‘yan sanda suka tambayi dattijo cewa a ina ya samo wannan gawar jariri? Sai ya amsa musu da cewa, ‘yarsa ce ta haifi jaririn kuma bai zo da rai ba, saboda haka ya ɗauke shi zai je ya binne a gida kamar yadda aka saba yi a zamanin baya.

Shike nan, ganin faruwar wannan lamari da kuma yadda ɓarawon nan ya fallasa kansa da cewa shi ɓarawon keke ne ba ɓarawon yara ba, sai dariya ta kama ‘yan sanda nan. Suna cikin dariyar nan, sai sauran masu laifin tuƙa keke ba tare da lasisi ba suka samu suka sulale, suka gudu.


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub