Zawarcin Ladan

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muƙyaƙyata: Zawarcin Ladan


A wani gari an taɓa yin wani limamin da matarsa ta addabe shi. Ya rasa yadda zai yi da ita, sai ya sake ta. Bayan ta yi idda, sai ladaninsa ya shiga zawarcin ta. Ana nan, ana nan, sai liman ya samu labari. Wata rana da aka yi sahun salla a masallaci, bayan ladan ya kira salla, an shiga masallaci ya tada iƙama, sai liman ya waigo ya ce: “A daidaita sahu don uban mutum”, sai ladan ya tambayi liman ya ce: "Liman ko da biyu ne?" Sai liman ya amsa da cewa: "Da goma ma don uban mutum".


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub