Shan Kunun Fulani

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muƙyaƙyata: Shan Kunun Fulani


Akwai wasu samarin Fulani su uku da suka zauna za su sha kunu a cikin ƙoƙo. Da suka zauna kamar yadda suka saba cin abinci, sai suka kewaye wannan ƙoƙo na kunu wanda yake rufe da faifai sannan kuma an ɗora ludayi a saman faifan.

Sai babbansu ya ɗauki ludayin sannan ya buɗe kunu ya fara sha. Ko da ya ɗebo kunun nan ya zuba a bakinsa sai ya ji zafi sosai, ashe kunun yana da zafi bai huce ba. Saboda haka sai ya fesar da kunun nan a jikin danga, sannan ya yi maza ya ce: “A jikin danga ake fesa ludayin fari, wannan ita she gadon gidanmu”. Sai ya miƙa wa na biyu ludayin.

Na biyun nan shi ma ya saka ludayi a cikin kunu ya kamfato ya zuba a bakinsa. Shi kuma da ya ji zafin har sai da hawaye ya zubo masa, amma haka ya daure ya shanye kunun nan. Ganin yana hawaye sai na farkon ya tambaye shi cewa: “Wane me ya saka ki hawaye ne?” Shi kuma sai ya amsa da cewa: “Wato lokashin dana  zuba kunun shan a baki sai na tuna mutuwar baffa, saboda haka sai kawai na fara kuka”. Sauran biyun suka jinjina masa. Sannan na uku ya kama.

Da na ukun nan ya kama ludayi, shima ya kamfato kunu ya zuba a bakinsa. Koda ya ji zafin kunun nan sai ya yi maza ya furzar da kunun sannan ya buɗe baki da ƙarfi ya ce: “Wutaaaaa…”

Daga nan sai sauran biyun suka tuntsure masa da dariya. Na farkon ya ce da shi: “Ɗan-bantan-uba, nima wutar na ji na furzar a jikin danga. Da ban yin haka ba da ba ku ɗanɗana ba”. Shima na biyun ya ce: “Nima wutar nan she ta saka ni hawaye. Babu wata mutuwa da na tuna. Da ban yi haka ai wallaci ba za ki ɗanɗana ba”.

Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub